Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta amince kan "ranar" da za ta tura dakarunta Jamhuriyar Nijar domin tunkarar sojojin da suka yi juyin mulki idan hanyoyin diflomasiyya suka gaza aiki.
ECOWAS ta jaddada cewa ba za ta kwashe lokaci mara iyaka tana tattaunawa da sojojin da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum ba.
Wadannan bayanai sun fito ne a karshen taron kwana biyu na shugabannin sojojin kasashen kungiyar ECOWAS da aka gudanar a Accra, babban birnin kasar gana, inda manyan jami'an suka fito da tsare-tsare na amfani da karfin soji kan sojojin Nijar.
ECOWAS ta ce amfani da karfin soji shi ne mataki na karshe da za ta dauka don warware rikicin siyasar da Jamhuriyar Nijar ta fada a cikin sakamakon juyin mulkin.
"Muna shirya tafiya (Nijar) kowane lokaci aka ba mu umarni," a cewar Kwamishinan ECOWAS kan Harkokin Siyasa, Tsaro da Zaman Lafiya Abdel-Fatau Musah yayin da yake jawabin kammala taron.
"An amince da ranar da za mu tafi kasar, wadda ba za mu bayyana ba."
Labari mai alaka: Amurka za ta bai wa Mohamed Bazoum taimako 'mara iyaka'
Ya kara da cewa har yanzu sun fi so a warware rikicin ta hanyar lumana.
"A yayin da muke wannan magana muna kuma shirya tawagar yin sulhu domin tafiya kasar. Don haka ba mu rufe kofar tattaunawa ba... (amma) ba za mu yi ta tattaunawa da ba ta da iyaka ba."
Kawo yanzu sojojin da suka yi juyin mulkin ba su ce uffan game da kalaman shugabannin tsaron kasashen na ECOWAS ba.