Wani gidan ajiye kayan tarihi a California da ke Amurka ya mayar da wasu kayayyakin sarauta guda bakwai ga masarautar Ashanti ta ƙasar Ghana a ranar Alhamis.
Hakan ya faru ne a yayin bikin farko na miƙa kayan tarihi na masarautar Ashanti da aka wawashe a zamanin mulkin mallaka.
Bikin ya zo ne a daidai lokacin da ake ƙara matsa lamba ga gidajen tarihi da cibiyoyi na ƙasashen Turai da Amurka kan su mayar da kayayyakin tarihi na Afirka da aka sace a zamanin mulkin da kasashen Birtaniya da Faransa da Jamus da kuma Belgium suka yi a Afirka.
Kayayyakin da aka dawo sun haɗa da sarƙoƙin wuya na zinare da kujerar ado ta zinare da dai sauransu, an kuma miƙa su ne a gaban manyan sarakuna a fadar Manhyia da ke birnin Kumasi.
Sarkin Ashanti Otumfuo Osei Tutu na biyu, wanda ke taka muhimmiyar rawa a masarautun Ghana, ya ce dawowar kayayyakin za ta taimaka wajen haɗa kan al'ummarsa.
"Abin da ya faru a yanzu ya tabbatar da irin abubuwan da suka wakana a shekarun da suka wuce lokacin da Birtaniya ta kawo mana hari tare da wawashe dukiyarmu," a cewar Sarkin.
"Mu kasance masu haɗin kai don samar da zaman lafiya da ci-gaba a masarautar nan," in ji shi.
Ivor Agyeman Duah, mai bai wa basaraken shawara, ya ce kayayyakin da aka dawo da su suna da matuƙar daraja.
"Dawowar kayayyakin gida na nufin wani muhimmin lokaci na alfahari ga masarautarmu," kamar yadda Duah ya shaida wa AFP.
Taron, wanda aka yi shi dab da cika shekaru 150 na yakin Anglo-Asante da ya wakana a shekarar 1874, ya haɗa shugabannin gargajiya da ƴan siyasa da jami'an diflomasiyya, waɗanda suka yi ado da tufafi masu ja da baƙi don nuna zaman makoki.
Kayayyakin da aka dawo su, suna daga cikin tarin kayayyakin da aka ajiye a gidan tarihi na Fowler da ke Amurka tun shekarar 1965.
Ba kamar sauran cibiyoyi da ke tattaunawa da Ghana ba, gidan adana kayan tarihi na Fowler bai sanya wani sharaɗi game da mayar da kayan ba.
"Wannan wani lokaci ne na musamman ga al'ummar Asante domin yana ƙarfafa danƙon zumunci a tsakaninmu da kakanninmu," a cewar masanin tarihin masarautar Ghana Osei-Bonsu Safo-Kantanka a yayin da yake zanta wa da kamfanin dillancin labarai na AFP a harabar fadar.
Za a baje kayayyakin a gidan ajiye kayan tarihi na fadar Manhyia a matsayin wani ɓangare na bikin da aka shirya yi na tsawon shekara.
Wannan matakin ya biyo bayan sanarwar baya bayan nan da gidan adana kayan tarihi na Birtaniya da gidan tarihi na Victoria da Albert da ke Landan suka fitar ta ba da aron kayayyakin tarihi na zinare da azurfa da aka wawashe daga masarautar Asante ga Ghana a wata yarjejeniya ta shekaru shida.
Ita ma maƙwabciyarta Nijeriya tana ci gaba da tattaunawa kan dawo da dubban kayan tarihinta da aka wawashe daga ƙarni na 16 zuwa 18 daga tsohuwar masarautar Benin waɗanda a halin yanzu suke gidajen tarihi da masu tattara kayayyakin tarihi a faɗin Amurka da Turai.
Shekara biyu da suka wuce, Benin ta karɓi wasu kayayyakinta masu daraja da kayan fasaha da sojojin mulkin mallaka na Faransa suka sace a shekarar 1892.