Gwamnatin Borno ta bayar da umarnin ga makarantu a jihar su rufe sakamakon ambaliya. / Hoto: Maine

Dubban mutane ne suka yi hijira daga gidajensu a wasu sassan Maiduguri a Jihar Borno da ke Nijeriya sakamakon ambaliyar ruwa.

Bidiyoyin da suka rinƙa yawo a shafukan sada zumunta sun nuna yadda ruwa ya shanye tituna, mutane na guduwa domin neman mafaka.

Dubban jama’a sun kwana a waje sakamakon yadda ambaliyar ta shanye musu gidaje.

Daga cikin wuraren da ambaliyar ta shafa har da Gidan Gwamnatin Borno da Fadar Shehun Borno da wasu sassa na Jami'ar Maiduguri da asibitin koyarwa na jami'ar da Kasuwar Monday

Ambaliyar wadda ta soma tun a makon da ya gabata, ta yi ƙamari a ranar Litinin da dare, inda aka wayi garin Talata mutane da dama sun shiga cikin wani hali.

Rahotanni sun nuna cewa ambaliyar ta faru ne sakamakon ɓallewar madatsar ruwa ta Alao da ke Ƙaramar Hukumar Konduga a Jihar Borno.

Muggan namun daji sun shiga gari

Hukumar kula da gidan ajiye namun daji ta Borno ta sanar da cewa sama da kaso 80 cikin 100 na dabbobin da ke cikin gidan sun mutu.

Shugaban gidan namun dajin Ali Abatcha ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

Shugaban ya yi gargaɗi kan cewa akwai muggan namun daji da suka fantsama cikin gari waɗanda suka haɗa da macizai da kadoji.

Rufe makarantu

Tun a ranar Litinin gwamnatin ta Borno ta umarci a rufe makarantu a jihar sakamakon take-taken da gwamnatin jihar ta gani na yiwuwar samun ambaliyar ruwan.

Sassan Nijeriya na ci gaba da fuskantar ambaliyar ruwa sakamakon mamakon ruwan sama da aka samu, wanda dama tuni hukumar hasashen yanayi ta ƙasar ta yi hasashen samun wannan ambaliya.

Ɗaruruwan mutane ne hukumar bayar da agajin gaggawa ta bayar da rahoton sun rasu a ƙasar sakamakon ambaliyar ruwan, jihohin Bauchi da Sokoto da Zamfara da Jigawa na daga cikin jihohin da ambaliya ta fi yi wa ɓarna a ƙasar.

TRT Afrika