Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun tunkari gidan da aka yi zargi mallakin magajin birnin Derna Abdulmonem al- Ghaithi ne / Hoto: Reuters

Daruruwan mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a birnin Derna na Libya ranar Litinin, suna masu zargin hukumomi da yin watsi da su bayan mummunar ambaliyar ruwa ta tagayyara su inda ta kashe dubban mutane.

Masu zanga-zangar sun taru a wajen babban masallacin Juma’a na kasar inda suka rika yin Allah wadai da majalisar dokoki da ke gabashin Libya da kuma shugabanta Aguilah Saleh.

Sun rika ihu suna cewa "Mutane suna so a rusa majalisar dokoki", "Aguila makiyin Allah ne", "Jinin wadanda suka yi shahada ba zai tashi a banza ba" da kuma "Dole a tsire barayi da maciya amana".

Sanarwar da aka fitar a madadin masu zanga-zangar ta yi kira a yi “gaggawar gudanar da bincike da hukunta wadanda ke da hannu a aukuwar bala’in” ambaliyar ruwan.

Labari mai alaka: Mutanen da ambaliyar ruwa ta kashe a birnin Derna na Libya za su iya kai wa 20,000

Sun bukaci a kafa ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Derna sannan a soma “sake gina birnin da kuma biyan mutane diyya” kana a binciki masu mulkin birnin da yadda suka kasha kudaden da aka sanya a karkashin kulawarsu.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun tunkari gidan da aka yi zargi mallakin magajin birnin Derna Abdulmonem al- Ghaithi ne sannan suka cinna masa wuta, a cewar wasu hotuna da aka wallafa a shafukan sada zumunta na Libya.

Gidan talbijin na Al-Masar ya rawaito cewa shugaban gwamnatin da ke da hedikwata a gabashin kasar, Oussama Hamad, ya soke majalisar gudanarwa ta Derna sannan ya bayar da umarni a gudanar da bincike a kanta.

‘Yan siyasa da masu sharhi sun ce rikicin da Libya ta fada tun bayan kifar da gwamnatin Muammar Gaddafi a 2011 ya sa an yi watsi da batun gina kasar da gyara gine-gine.

Ranar 10 ga watan Satumba, wasu manyan madatsun ruwa biyu da tun a 1998 aka bayar da rahoton lalacewarsu, suka fashe sakamakon mahaukaciyar guguwa mai hade da ruwan sama da aka sanya wa suna ‘Daniel’ wadda ta rikirkita gabashin Libya, musamman birnin Derna mai dauke da kimanin mutum 100,000.

Ta kashe akalla 3,330 sannan dubbai sun bata. Hasalima magajin birnin ya ce kiyasi ya nuna cewa wadanda suka mutu za su iya kai wa 20,000.

Dubban mutane suna cikin dimuwa da matukar bukatar taimakon abinci da sauran abubuwan bukata, a yayin da ake fargabar barkewar cutukan da suka hada da kwalara da amai da gudawa, kamar yadda hukumomin Majalisar Dinkin Duniya suka bayyana.

Tuni kasashe irin su Turkiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa da sauransu suka soma kai wa kasar ta Libya tallafi.

Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta ce tana bukatar fiye da dala miliyan 71 don taimaka wa wadanda ke cikin mawuyacin hali bayan mummunar ambaliyar ruwa ta mamaye Libya.

TRT Afrika da abokan hulda