Ambaliya a Liberia za ta iya raba mutane da muhallansu da kuma ƙarancin abinci.  / Hoto: Getty Images      

Daga Foday Couch Bayoh

A cewar ofishin Hukumar Majalisar Dinkin Duniya Mai Kula Da Harkokin Jinkai (UNOCHA), ambaliya na ta'azzara matsalolin al'ummomi masu rauni, su ƙara sa wa batutuwa kamar rashin wadataccen abinci, da rashin abinci mai gina jiki,da rashin kwanciyar hankali da kuma tashin hankali su ƙara taɓarɓarewa.

Wani nazarin hukumar UNOCHA a kan yanayin ambaliya a Afrika ta Yamma da ta Tsakiya a watan Satumban 2023 ya nuna cewa, ambaliya ba tana taƙaita ga cutarwa ta nan-take ba ne kaɗai, har ila yau, tana da illa ta dogo lokaci a kan tsaftar jiki, da tsaftar muhalli da kuma a kan jama'a.

Ambaliyar ruwa na nuni da mummunan tasirin ayyukan ɗan'adam a kan muhallin da kuma gazawar manufofi, saboda haka yake zama mai ta'azzara matsaloli wa al'ummomin da tuni suna fama da ɗimbin matsaloli. Har ila yau, ambaliya tana da mummunan tasirin a kan gine-gine da kuma hanyoyin neman abinci.

Majalisar Dinkin Duniya ta rawaito cewa, a faɗin Afrika, matsalar ɗumamar yanayi na kankama, tana haifar da kassara hanyoyin neman abinci, da kawo cikas a kan samar da wadataccen abinci, da ta'azzara tashe tashen hankali saboda albarkatu ƙalilan da kuma raba mutane da yawan gaske da muhallansu.

Liberia za ta iya koyi da abin da ya samu wasu ƙasashen har suka ɗauki matakan hana afkuwar mummunar ambaliya.

A baya bayan, Lardin Yammacin Cape, da ya haɗa da Cape Town, ya yi fama da mananan ambaliya da suka halaka aƙalla mutane 11 bayan an kwashe kwanaki ana tafka ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.

Ethiopia da Somalia sun fuskanci ambaliya a watan Maris 2023, abin da ya kai ga ritsawa da gwamman mutane Sannan ya shafi mutane 300,000, kamar yadda Hukumar Majalisar Dinkin Duniya Mai Kula Da Harkokin Jinkan Bil Adama (UNOCHA) ya rawaito.

Waɗannan munanan yanayin su yi ɓarna kan gidaje da dabbobi a yankunan karkara, waɗanda har yanzu ke kan farfaɗowa daga farin na kusan kimanin shekaru uku, da ya jefa yankin cikin matsalar yunwa mafi muni a cikin gwamman shekaru.

A shekarar 2022, Najeriya ta yi fama da ambaliyar da ta taɓa yi mafi muni a cikin gomman shekaru, wacce ta raba miliyoyin mutane da muhallansu sannan ta haddasa babbar asarar tattalin arziki.

Ɗaya daga cikin ambaliya mafi muni a Afrika ta faru a Libya a ranar 11 ga watan Satumbar wannan shekarar, ta halaka dubban mutane sannan ta lalata gine-gine.

Hukumar UNHCR ta yi kiran gaggawa game da buƙatun mutanen da suka rasa muhallansu sama da miliyan 3.4 da kuma al'ummomin da suka ba su masauki, sakamakon mummunan ambaliya a ƙasashe Afrika da dama, da suka haɗa da Najeriya, da Chadi, da Nijar, da Burkina Faso, da Mali da kuma Kamaru.

Ambaliyar Liberia ta yi awun gaba da kayayyakin gida da suka haɗa da ajiyayyen abinci, ta ƙara ta'azzara matsin tattalin arziki./Hoto Reuters

Tasirin hakan kan kiwon lafiya babba ne, yayin da ruwan sama ke ƙara yiwuwar kamuwa da ɓullar annobar amai da gudawa. Alal misali, Malawi da ke fama da ɓullar annobar amai da gudawarta mafi muni, ta fuskantar ƙarin ƙalubale saboda ƙaruwar ruwan sama da ke kawo cikas ga ƙoƙarin da a ke yi na shawo kan cutar.

Har wa yau, Madagascar, wacce ba a samu wanda ya kamu da cutar amai da gudawa a cikinta tun shekarar 2000 ba, ta yi fama da ƙaruwar annobar, biyo bayan faruwar mummunar guguwa da kuma ambaliya.

Dr. Matshidiso Moeti, Darakta Mai Kula Da Afrika a Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO), ya ce, abubuwa da suka shafi mummunan yanayi da kuma tashin hankali, waɗanda ke tozarta mutane masu rauni,su suke ƙara ta'azzara annobar amai da gudawa da ake fama da ita a halin yanzu a Afrika.

Yanzu Liberia ta samu kanta a yanayin da za a iya kwatanta ta da wata. A watan Satumban 2023, ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya shafi birane daban-daban, mafi munin ambaliya an rawaito ta faru ne a gundumomin arewaci maso gabashi na Grand Cape Mount, da Bong da kuma Montserrado.

Yankuna kamar New Kru Town, da Gbarnga City da kuma ɓangaren birni na Monrovia da kewaye, musamman lamarin ya shafe su sosai.

A cewar ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa na Red Cross da Red Crescent (IFRC), ambaliyar cikin gari da ta gaɓar teku ta shafi kimanin mutane 15,200 kuma ta lalata gine gine da kuma al'ummomi masu kamun kifi.

Sashen Hasashen Yanayi Na Hukumar Sufuri Ta Liberia ya yi hasashen cewa, za a yi ruwa babu ƙaƙƙautawa a watannin Satumba da Oktoba na 2023 a faɗin ƙasar, abin da ke ƙara fargabar ƙarin ambaliya da abin da ke biyo bayanta.

In ji Ƙungiyoyin IFRC, yayin da kawo yanzu ba a rawaito rasa rai ba, amma iyalai da dama da abin ya ritsa da su sun rasa muhallansu, suna neman wajen fakewa a gine gine-ginen gwamnatin ko gidajen abokanai da na dangi.

Ambaliyar ta yi awun gaba da kayayyakin gida da suka haɗa da kayan abinci, abin da ya ƙara tsadar rayuwa.

Wajibi ne Liberia ta ɗauki ƙwararan matakan magance wannan matsalar mai ci gaba da ƙaruwa. Sauyin yanayi, da zama a yankin da ambaliya za ta iya faruwa, da tsakanin talauci da kuma wasu matsaloli masu nasaba da tattalin arziki da zamantakewa suna bayyana rauninsu.

Kiran da Shugaban Ƙasa George Weah ya yi, yayin Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya na 2023, ya bayyana ƙarara buƙatar gaggawa da ake da ita, ta a haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen magance matsalolin sauyin yanayi.

Ambaliyar ruwa a Liberia za ta iya haddasa rabuwar mutane da muhallansu, da ƙarancin e, da ƙarancin tsaftataccen ruwan sha da kuma matsalolin tsaftar muhalli da sauransu.

A watan Agusta na shekarar 2007, ambaliya ta raba ɗaruruwan mutane da muhallansu, kuma ta katse hanyar samar wa mutane 250,000 a Monrovia a 2007, a cewar Hukumar IRIN ta Majalisar Dinkin Duniya.

Shekara ɗaya tsakani, Hukumar IRIN ta rawaito cewa, Monrovia ta yi fama da ambaliya mafi muni bisa alƙaluma, sakamakon mamakon ruwan sama mai karfin gaske, abin da ya yi sanadiyar rasa muhallin mutane kimanin 1,000, a cewar mahukuntan Liberia.

Duk da wanzazzun manufofi a kan shiryawa da tunkarar bala'i, amma ba a yi wani abun ku-zo-mu-gani ba, wajen hana bala'i shafe cigaban da aka samu wajen cim ma Muradun Ɗorewar Cigaba ba.

Wajibi ne Liberia ta muhimmantar da hana faruwar ambaliya, ba mayar da martani ba kaɗai. Ya kamata a ilmantar da ƴan ƙasa game da abubuwan da ke haddasa ambaliya da kuma yadda za a magance ta, da ya haɗa da kwashe kwatami da kuma wasu ayyukan gyare gyare.

Hasashen a kan ambaliya yana da muhimmanci, amma Afrika na fuskantar ƙalubale ta wannan janibin, saboda da ƙarancin bayanai da kuma tashin wadatattun ayyukan da suka gabata da za a yi koyi da su.

Ya kamata Liberia ta sama wa al'ummomi bayanai game da sauyin yanayi a matsayin wani matakin riga-kafi, da kuma inganta ƙwazo a jerin ayyuka.

Ya kamata a rungumi tsarin yin gargaɗi a kan ambaliya kamar GloFAS. Bugu da ƙari, yana da muhimmanci a bunƙasa tattalin arzikin al'ummomi, har da raba ƙafa a hanyoyin samunsu.

Wajibi ne a samu aniyar siyasa da za ta tabbatar Liberia ta samu madogara wajen yaƙi da ambaliya,ta hanyar kyautata manufofi da kuma aiwatar da su.

Tilas ne Liberia ta yi koyi da da abin da ya faru a sauran ƙasashe kuma ta yi azama wajen katse kasadar yiwuwar afkuwar ambaliya wadda Sashen Hasashen Yanayi na Hukumar Sufuri Ta Liberia na watan Satumba da Oktoba 2023 ta sanar.

Tunda ambaliya sakamako ne na wasu aikace-aikacen ɗan adam da ke shafar yanayi, da kuma gazawar manufofi, da aikin ɗan adam kamar sare bishiyoyi da ƙarancin shirin amfani da ƙasa, wajibi ne a magance su.

Ambaliya ba ɓarna ta nan take ta ke yi ba kaɗai; tana da illa ta dogon lokaci, musamman ta bangaren kiwon lafiyar jama'a, abin da ke tsawaita wahalhalun al'ummomin da abin ya shafa.

Idan aka yi la'akari da abubuwan da sauran ƙasashen Afrika suka yi fama da su a baya bayan nan, da kuma ita ma wanda ta yi fama da shi, tilas ne Liberia ta saurari wannan jan hankalin.

Foday Couch Bayoh, Jr. ƙwarararre ne a fannin Shugabanci da Ci-gaba tare da sha'awa a ɓangaren Shugabancin Duniya da Ci-gaban ƙasa da ƙasa, da kuma Haɗewar Yankuna da Siyasar Tattalin Arziki Da Ɗorarren Ci-gaba Da Aiki Bisa Doka.

Hattara: Ra'ayin da marubucin ya bayyana ba dole ba ne ya zo ɗaya da ra'ayin, hange da kuma manufofin tace labarai na TRT Afrika.

TRT Afrika