An buɗe rumfunan zaɓe tun da ƙarfe 8 na safe. / Hoto: AFP

Tunisia na gudanar da zaɓen shugaban ƙasa yau Lahadi, inda babu ƙwaƙƙwaran ɗan takarar da ke ja da shugaba Kais Saied, wanda ake ganin zai lashe zaɓen. Manyan masu sukarsa, ciki har da babban ɗan takara, duka an ɗaure su.

Ƙasar da ke Arewacin Afirka tana alfahari da cewa ita ce inda aka fara guguwar sauyi ta zanga-zangar Arab Spring, sama da shekaru 1 da suka wuce.

An buɗe rumfunan zaɓe da ƙarfe 8:00 na safe (7 agogon GMT) kuma za a rufe da ƙarfe 6:00 na yamma (5 agogon GMT). Sakamakon farko zai zo kafin ƙarshen Laraba ko ma gabanin haka, cewar hukmar zaɓe ta ISIE.

Kafin ranar fara kaɗa ƙuri'a, ba a yi gangamin zaɓe ko muhawarar 'yan takara ba, sannan kusan duka fastocin yaƙin neman zaɓe a titunan birni na Saied ne.

Yayin da ake ganin ƙarancin yiwuwar samun sauyi a ƙasar da ke fama da matsin tattalin arziƙi, yanayin fatan masu zaɓe ya yi kama da na yanke ƙauna.

Ɗaure 'yan adawa

"Ba mu da wata alaƙa da siyasa," cewar Mohamed, mai shekaru 22, wanda ya ambaci sunansa zalla saboda tsoron hukunci, yayin zantawarsa da AFP a Tunis. Ya ce shi da abokansa ba su da niyyar kaɗa ƙuri'a.

Bayan hawansa kujerar mulki a zaɓen 2019, Saied mai shekaru 66, ya jagoranci sake rubuta tsarin mulkin ƙasar. Gabanin zaɓen na Lahadi, an yi amanna cewa yana da goyon bayan rukunin al'ummar ƙasar ma'aikata.

Sai dai kuma, wasu daga cikin masu sukarsa a duka ɓangarorin siyasa an ɗaure su, wanda ya haifar da suka daga cikin gida da waje.

Jagororin adawa da aka ɗaure sun haɗa da Rached Ghannouchi, shugaban jam'iyyar adawa ta Ennahdha, wadda ta samu fifiko a siyasar ƙasar bayan juyin juya-hali.

An kuma ɗaure Abir Moussi, shugaban jam'iyyar Free Destourian Party, wadda masu suka ke cewa yana ƙoƙarin dawo da shugabannin da aka kawar a 2011.

'Tururuwar fitowa'

Hukumar zaɓe ta ISIE ta ce kusan mutane miliyan 9.7 ake sa ran za su fito zaɓen, amma ganin yadda ake sa ran shugaba Saied ne zai lashe zaɓen, da kuma tarin matsalar tattalin arziƙi ba ta haifar da karsashin fita zaɓe ba.

Masu takara da Kais Saied su ne tsohon ɗan majalisa Zouhair Maghzaoui, wanda ya goyi bayan Saied a kamfen ɗin sauya tsarin mulki na 2021, da kuma Ayachi Zammel, wani ɗan kasuwa da bai yi suna ba, wanda yake kurkuku tun bayan da hukumar zaɓe ta amince da aniyarsa ta shiga takara a watan jiya.

A wani jawabi ranar Alhamis, Saied ya yi kira da a yi "tururuwar fitowa zaɓe" don su kawo zamanin "sake gina ƙasa".

Ya ambaci "daɗaɗɗen yaƙi kan dakarun munafukai masu alaƙa da ƙasashen waje", waɗanda ya zarga da cewa "sun shiga yawancin hukumomin gwamnati, suna rusa ɗaruruwan ayyuka" ƙarƙashin gwamnatinsa.

TRT Afrika