Shugaban Tunisia Kais Saied ya kori Ministan Harkokin Addini Ibrahim Chaibi daga muƙaminsa bayan gomman Mahajjata sun rasu a yayin Aikin Hajji.
A wata sanarwa da Fadar Shugaban Tunisia ta fitar, ba ta bayyana ainahin dalilin sallamarsa ba, sai dai korar na zuwa ne a daidai lokacin da aka samu mutuwar Alhazan ƙasar 49 a Saudiyya.
Chaibi a ranar Juma'a kafin korarsa ya sanar da cewa akasarin 'yan Tunisia da suka mutu sun tafi Saudiyya ne da bizar yawon buɗe ido ba ta shirin Aikin Hajji na ƙasar ba.
An ta caccakar Chaibi a kafafen sada zumunta inda ake zarginsa da wallafa hotunansa yana Aikin Hajji a daidai lokacin da Alhazan ƙasar ke mutuwa.
AA