Hukumomi da kungiyoyi masu zaman kansu sun jima suna yaki da tsallaka teku ba bisa ka'ida ba. Photo/Getty Images

Akalla ‘yan ci-rani 23 suka bace, hudu kuma suka rasu a ranar Asabar bayan kwale-kwalensu biyu sun nutse a kusa da Tunisia a daidai lokacin da suke kokarin tsallake tekun Mediterranean zuwa Italy.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa masu gadin teku sun ceto wasu mutum 53 a kusa da birnin Sfax, inda mutum biyu suna cikin mawuyacin hali, kamar yadda alkalin kotun Sfax Faouzi Masmoudi.

A ‘yan makonnin nan, gwamman mutane sun bace wasu kuma sun mutu sakamakon hatsarin kwale-kwale a kusa da Tekun Tunisia.

Tunisia ta zama wata tasha da masu tafiya ci-rani ke bi domin tsallakawa Turai a maimakon Libya da suke bi a baya.

A kwanakin baya an ta kama masu safarar bil adama a Libya wanda hakan ya sa ake ganin suka karkata zuwa Tunisia.

Masu gadin teku a ranar Juma’a sun bayyana cewa sama da ‘yan ci-rani 14,000 wadanda akasarinsu daga nahiyar Afrika suke aka kama su ko kuma aka ceto su a rubu’in farko na wannan shekara.

Wannan adadin ya ninka sau biyar kan adadin da aka samu a irin wannan lokaci a bara, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana.

Ministan harkokin waje na Tunisia Nabil Ammar ya ce kasarsa na bukatar kudade da kuma kayayyakin aiki domin kare iyakokinta.

Reuters