An harbe shugaban ƴan adawar Tunisia Chokri Belaid a 2013. / Hoto: Getty Images

An yanke wa wasu mutum huɗu hukuncin kisa sannan an yanke wa biyu hukuncin ɗaurin rai da rai kan samunsu da laifin kisan shugaban yan adawan Tunisia Chokri Belaid a 2013.

Mataimakin babban mai shigar da ƙara na hukumar shari’a mai yaƙi da ta’addanci ne ya sanar da hakan a ranar Laraba.

Haka kuma an yanke wa wasu mutanen waɗanda aka kama da laifi hukuncin ɗauri daga shekaru biyu har zuwa shekara 120, sannan an wanke mutum biyar daga zarge-zargen da ake yi musu inda aka sallame su.

Har yanzu Tunisia na yanke hukuncin kisa, musamman kan laifukan ta’addanci, duk da dakatarwar da aka yi na yanke irin hukuncin a 1991.

Ƴan ta’adda waɗanda suke da alaƙa da Daesh sun yi iƙirarin kashe Belaid da kuma Mohamed Brahmi bayan wata shida, wanda shi ma ɗan adawa ne.

Hukumomi a 2014 sun kashe Kamel Gadhgadhi a wani samame na farautar ƴan ta’adda, wanda shi ne wanda ya kitsa kashe Belaid.

Belaid da Brahmi dukkansu sun kasance masu sukar Ennahda, jam'iyyar da ta mamaye siyasar Tunisiya da rinjayen majalisar dokoki tsawon shekaru goma bayan boren Tunisia a shekara ta 2011.

Tasirin jam’iyyar ya ragu a watan Yulin 2021, lokacin da Shugaba Kais Saied ya karbi ragamar mulki.

TRT Afrika da abokan hulda