Turkiyya ta miƙa ta'aziyyarta kan waɗanda suka rasu sakamakon mummunan haɗarin jirgin ruwa a Nijeriya.
“Mun yi matuƙar baƙin ciki da rashin rayuka da aka samu bayan nutsewar jirgin ruwa da ke ɗauke da fasinjoji kimanin 300 a Nijeriya,” in ji M'aikatar Harkokin Waje ta Turkiyya a wata sanarwa ranar Juma'a.
Ma'aikatar ta miƙa ta'aziyyarta ga al'umma “'yan uwa kuma abokai” da ke Nijeriya.
Jirgin ruwan yana ɗauke da mutane 300 da ke dawowa daga taron addini yayin da jirgin ya kife, a jihar Neja da ke arewa ta tsakiya a daren Talata.
Gano gawarwaki
Aƙalla gawarwaki 60 aka gano yayin da aka ceto mutane 160 bayan afkuwar haɗarin, cewar wani jami'i ranar Laraba.
Haɗarin na Kogin River Niger ya faru a wuraren Al'ummar Gbajibo, in ji Jibril Abdullahi Muregi, shugaban ƙaramar hukumar Mokwa. An kwaso gawarwaki da dama ranar Juma'a yayin da ake ci gaba da aikin ceto.
Fasinjojin, yawancinsu mata da yara, suna kan hanyarsu ta zuwa bikin Maulidi.
Hukumomi sun ce an samo ƙarin gawarwaki ranar Juma'a, kuma ana ci gaba da aikin ceto, kwanaki bayan afkuwar haɗarin.