Masu gadin teku na kasar Tunisia sun ce sun gano kusan gawarwaki 210 na ‘yan ci-rani a kasa da mako biyu wadanda ruwa ya jawo zuwa gabar tekun kasar.
Gano gawarwakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun karuwar masu yunkurin tsallaka teku zuwa Turai.
Binciken wucen gadi da aka gudanar kan gawarwakin ya nuna cewa jama’ar da suka rasu sun fito ne daga nahiyar Afrika, kamar yadda masu gadin tekun ska sanar.
Cikin gawarwaki 210 da aka gano a kasa da mako biyu tun daga 18 ga watan Afrilu, sama da 70 an gano su ne daga gabar teku da ke gabashin Sfax da tsibiran Kerkennah da Mahdia masu makwaftaka, kamar yadda hukumomi suka bayyana.
Wadannan wuraren uku dai sun kasance wuraren daura niyyar tafiya zuwa tekun Italiya, ciki har da tsibirin Lampedusa da ke can gaba.
Adadin gawarwakin ‘yan ci-rani na so ya fi karfin dakin ajiye gawarwaki na asibitin Habib Bourguiba wanda ke cin gawarwaki 30 zuwa 40.
Wahalar binne ‘yan ci-rani
Domin rage matsin lamba ga asibitoci, hukumomi na bayar da himma wurin gaggauta binne gawarwakin bayan gudanar da gwajin kwayoyin halitta ko kuma idan ‘yan uwa suka gane gawarwakinsu.
Romdhane Ben Amor, wanda shi ne mai magana da yawun wata kungiya ta kare hakki a Tunisia da ke mayar da hankali kan matsalolin ‘yan ci-rani ya ce a bara hukumomi sun ce za su samar da wata makabarta domin ‘yan gudun hijira, “kan cewa su ba Musulmai ba ne.”
Amma Amor ya ce duk da haka babu makabartar wanda hakan yake jawo cikas wurin samar da wuraren binne su.