Aljeriya ta ki amincewa da bukatar Faransa ta amfani da sararin samaniyarta wajen kaddamar da duk wasu ayyukan soji a Jamhuriyar Nijar, kamar yadda gidan rediyon kasar ya fada a ranar Litinin da marece, bayan juyin mulkin da aka yi a Niijar din wacce ta hada iyaka da Aljaeriya, ranar 26 ga watan Yuli.
Aljeriya ta ce tana adawa da kowane irin hari daga sojojin wata kasar waje zuwa Nijar kuma ta fi son a bi matakin diflomasiyya don mayar da doka da oda, a cewar gidan rediyon.
Faransa tana da dakaru 1,500 a Nijar wadanda aka jibge a sansaninta a watan da ya gabata. Aljeriya ba ta fayyace me take nufi da ayyukan sojin da take nufi ba.
A makon da ya gabata Kungiyar Cigaban Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka ta (ECOWAS) ta amince kan tsayayyiyar ranar da za a afka wa Nijar matukar aka gaza warware rikicin ta hanyar diflomasiyya - lamarin da zai iya dagula yanayin da ake ciki a yankin da yaki da talauci suka tagayyara.
Aljeriya ta sha nanata cewa tana adawa da duk wani katsalandan din sojojin kasashen waje a yankin Sahel, inda take tsoron barkewar rikicin da zai iya haddasa kwararar 'yan gudun hijira a kan iyakarta, wata majiya mai alaka da gwamnati ta shaida wa Rueters.
"Muna adawa da juyin mulki amma muna kuma adawa da daukar matakin soji da zai munana al'amarin da zai shafi wajen yankin Sahel," majiyar ta shaida wa Reuters.
Mahukuntan Faransa ba su amsa bukatar da aka mika musu ta neman su ce wani abu ba.