Al-Burhan ya kasance yana jagorantar sojojin Sudan a yakin da suke yi da RSF. / Hoto: Others

Shugaban Sojin Sudan Abdel Fattah al-Burhan ya sha alwashin ci gaba da yakin suke yi da rundunar RSF a kasar, inda ya yi watsi da bukatar tsagaita wuta ta baya-bayan nan.

A farkon makon nan ne Shugaban RSF Hamdan Dagalo ya amince da bukatar tsagaita wuta wadda kungiyoyin farar hula suka gabatar, wanda hakan ya kunshi idan sojoji sun amince.

Sai dai masu lura da al’amura sun mayar da martani cikin kakkausar murya bisa la’akari da alkawuran da rundunar ta yi a baya da ba ta cika ba.

Bangarorin biyu sun cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta da dama a farkon watannin yakin. Sai dai masu ido sun mayar da martani cikin kakkausar murya bisa la’akari da alkawuran da rundunar ta yi a baya wadanda ba ta cika ba.

Bangarorin biyu sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da dama wadanda ba su dore ba a farkon watannin yakin.

“Duka duniya ta shaida yadda dakarun ‘yan tawayen nan suka rinka aikata laifukan yaki da kuma laifin take hakkin bil adama a Yammacin Darfur da sauran yankunan Sudan. Sakamakon haka, ba za mu sasanta da su ba, ba mu da wata yarjejeniya da su,” kamar yadda Burhan ya bayyana, wanda shi ne shugaban na Sudan a lokacin da dakarunsa suka taru a birnin Port Sudan.

‘Mai cin amana, matsoraci’

An soma wannan yakin a ranar 15 ga watan Afrilu inda ya lalata wurare masu yawa a Sudan da kuma raba da sama da mutum miliyan 7.5 da muhallansu.

Ganin cewa RSF ta samu dama a wannan yakin, Kungiyar Intergovernmental Authority on Development, ta samu Burhan da Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti, a watan da ya gabata, don amincewa da wani taron kai tsaye.

Sai dai Burhan a ranar Juma’a ya yi watsi da hakan inda ya kira abokin adawar tasa a matsayin “sakarai”, “mai cin” kuma “matsoraci”.

Ya yi watsi da bukatar tsagaita wutat da Dagalo ya saka wa hannu a Addis Ababa babban birnin Habasha a wannan makon.

Haka kuma Burhan ya caccaki shugabannin Afirka wadanda suka hada da Habasha da Kenya wadanda suka karbi Dagalo a wata ziyara da ya kai a makon nan da kuma wasu ‘yan siyasar Sudan wadanda suka hadu da shi a Habasha.

Reuters