Abu ne ruwan dare a Afirka ta Kudu a yi amfani da sojoji a cikin kasar wajen magance wata matsala. Hoto: Reuters

Shugaban Kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya bayar da umarnin amfani da sojoji 3,300 don yaki da masu hakar ma'adinan kasa ba bisa ka'ida ba, in ji wata sanarwa da aka fitar daga ofishinsa a ranar Alhamis din nan.

Ma'aikatar Tsaron Kasa ta Afirka ta Kudu (SANDF) za ta aiwatar da shirin amfani da sojoji ne, wanda zai lakume dala miliyan 26, don tabbatar da doka da oda karkashin "Farmakan Habaka", in ji sanar da kakakin Ramaphosa, Vincent Magwenya ya fitar.

A shekarar 2019 ma an taba aika SANDF zuwa lardin Yammacin Cape don yaki da wata kungiyar masu tayar da kayar baya.

Fadar shugaban kasar ta kuma ce "Mambobin SANDF za su ci gaba da hadin gwiwa da 'yan sandan Afirka ta Kudu, su kaddamar da farmakin yaki da muggan laifuka kan masu hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba a lardunan kasar, daga 28 ga Oktoban 2023 zuwa 28 ga Afrilun 2024."

Hukumar Kula da Hakar Ma'adanai ta Afirka ta Kudu ta ce ana hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba a wuraren da aka daina amfani da su da wadanda ake tsaka da amfani da su, lamarin da ke dakushe karsashin masu zuba jari da ka iya zuwa kasar.

Hukumar ta kuma ce hakar ma'adinan ba bisa ka'ida ba na janyowa kamfanoni asarar rand biliyan bakwai, yayin da tattalin arzikin kasar kuma ke asarar gomman biliyoyin rand da za a iya samu idan aka fitar da ma'adinan zuwa kasashen ketare.

TRT Afrika