Dakarun Afirka ta Kudu za su kwashe shekara ɗaya a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo,/Hoto: Rundunar Tsaron Afirka ta Kudu/X

Afirka ta Kudu za ta tura dakaru 2,900 a matsayin tallafinta ga Ƙungiyar Ci-gaban Ƙasashen Kudancin Afirka (SADC) wadda za ta aika sojoji domin kawar da ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, a cewar wata sanarwa da ofishin shugaban ƙasar ya fitar ranar Litinin.

Dakarun za su kwashe shekara ɗaya daga 15 ga watan Disamba na 2023 zuwa 15 ga watan Disamba na 2024, kuma za su laƙume kusan ran biliyan biyu, kwatankwacin dala miliyan 105.75, in ji sanarwar.

A watan Mayun da ya gabata ne Ƙungiyar Ci-gaban Ƙasashen Kudancin Afirka (SADC) mai mambobi 16 ta amince ta tura dakaru Kongo, ƙasa mafi arzikin ma'adanin kwalbat (cobalt) kuma wadda ta fi yawan ma'adanin kofa (copper) a Afirka, domin shawo kan rikicin da ke faruwa a gabashin ƙasar.

An kwashe shekara da shekaru ana gwabza yaƙi tsakanin ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da dakarun gwamnatin a gabashin Kongo lamarin da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba fiye da mutum miliyan 7 da muhallansu.

An bai wa dakarun SADC umarnin taimaka wa dakarun gwamnatin ƙasar a yaƙin da suke yi da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai. Dakarun ƙasashen Malawi, Afirka ta Kudu da Tanzania ne suke ƙarkashin wannan tawaga.

An aika dakarun ne a yayin da Kongo ke fafatawa da ƙungiyar an tawaye ta M23 ta ƴan ƙabilar Tutsi wadda mayaƙanta ke zafafa kai hare-hare a baya bayan nan tare da yin barazana ga Goma, babban birnin Arewacin Kivu.

Reuters