Kambin Sarautar Birtaniya / Hoto: Getty  Images / Photo: Getty Images

Wasu 'yan Afirka ta Kudu sun yi kira ga Birtaniyya da ta mayar musu da dutsen Daiman dinsu mafi girma a duniya, wanda aka fi sani da Tauraron Afirka, da aka sanya a cikin sandan Sarautar da Sarki Charles na Uku zai rike a bikin nadin sarautarsa a ranar Asabar.

Daiman din mai nauyin karat 530, an gano shi ne a kasar Afirka ta Kudu a shekara ta 1905, daga nan gwamnatin Birtaniya wacce ta yi wa kasar mulkin mallaka a wannan lokacin ta mika shi ga masarautarta, a cewar wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya fitar.

A yanzu da duniya ke ci gaba da tattaunawa game da mayar da da kayayyakin fasaha da kayan tarihi da aka sace a lokacin mulkin mallaka, wasu 'yan Afirka ta Kudu na kira da a dawo musu da dutsen daiman dinsu.

"Ya kamata a dawo da daiman din 'yan Afirka ta Kudu, domin ya kamata ya zama wata alama ta alfaharinmu da al'adunmu da kuma zama wani abu da muka gada," in ji Mothusi Kamanga, lauya kuma mai fafutuka a Johannesburg wanda ya gabatar da kara ta yanar gizo ya kuma samu goyon baya na kusan mutum 8,000 da ke neman a mayar da daiman din.

Ina ganin gaba daya al'ummar Afirka sun fara fahimtar cewa yanke mulkin mallaka ba wai kawai a bar mutane su samu 'yanci ba ne, amma har da a dawo da abin da aka kwace daga hannunmu."

Diaman din da aka fi sani da Cullinan a hukumance, an cire shi ne daga nau’in dutsen Cullinan karat 3,100 da aka hako shi kusa da Pretoria.

An sanya wani dan karamin bangare na dutsen diaman din a cikin kambin da sarakunan Birtaniya ke sawa a lokutan bukukuwa tare da sandar da su ke rikewa, ana ajiye su ne tare da sauran kayan ado na kambi a cikin Hasumiyar London.

An sanya Kwafin Daiman din Cullinan gaba daya, wanda ya kai girman hannun mutum a gidan adana kayan tarihi da ke Cape Town.

"Na yarda kan cewa a dawo da shi gida domin a karshe dai sun karbe daga wajenmu a lokacin da suke zaluntarmu," in ji Mohamed Abdulahi mazaunin Johannesburg.

Wasu kuma sun ce ba su da karfin gwiwa game da hakan.

"Ba na jin yana da wani amfani kuma. Abubuwa sun canza, muna ci gaba," in ji Dieketseng Nzhadzhaba mazaunin yankin.

"Abin da ya dame su a zamanin da kan zama masu iko da fifiko ... ba damuwar mu ba ne a a yanzu."

TRT Afrika