James Ibori ya taba yin zaman kurkuku a Birtaniya bayan wata kotu ta kama shi da laifi./Hoto:Reuters

Ƙungiyoyin fararen hula na Birtaniya da Nijeriya sun nemi gwamnatin Birtaniya da ta mayar wa Nijeriya da kuɗaɗen da aka ƙace daga hannun tsohon gwmanan Jihar Delta James Ibori, wanda aka kama shi da laifin sace kuɗaɗen gwamnati, ta yadda kuɗaɗen za su amfani 'yan Nijeriya.

A wata wasiƙa da suka aike wa ministocin harkokin cikin gida na Birtaniya da na harkokin waje na Nijeriya, gamayyar mai ƙungiyoyi 50 sun ce salon yadda ake jan dogon lokaci a tsarin mayar da kuɗaɗen, yana yin zagon-ƙasa ga ƙaƙƙarfan saƙon yaƙi da cin hanci da ake so a nuna kan lamarin Ibori, wanda aka shafe fiye da shekara 10 ana shari'arsa.

"Shekarun da aka shafe ana wannan dambarwar da kuma batun mayar da waɗannan ƙadarorin na sata na nufin zuwa yanzu ƴan Nijeriya za su fara tantamar batun yaƙin da ake yi da cin hanci," in ji wasiƙar, wacce ɗaya daga cikin waɗanda suka sanya hannu a kanta ya yaɗa ta a ranar Alhamis.

Ibori, wanda tsohon gwamnan Jihar Delta mai arzikin man fetur ne a Kudancin Nijeriya, ya amsa laifi kan tuhuma 10 da ake masa kan halasta kuɗin haram a wata kotu a Landan a shekarar 2012, inda aka yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 13 a gidan yari, inda ya yi rabin wa'adin kafin daga baya a sake shi ya koma gida.

Ibori wanda har yanzu yake da faɗa a ji a Nijeriya, ya ziyarci Shugaba Bola Tinubu a baya-bayan nan, kuma yana da abokai a madafun ikon ƙasar.

Labari mai alaka: Kotun Birtaniya ta ba da umarnin kwace fam miliyan 101 daga hannun James Ibori

Ƙungiyoyin, waɗanda suka haɗa da Transparency International da Africa Network for Environment and Economic Justice, sun ce kamata ya yi a yi amfani da kuɗaɗen da aka ƙwato ɗin wajen yin ayyukan da za su amfani al'ummar Jihar Delta kuma ya kamata a yi hakan ƙarƙashin sa idon ƙungiyoyin fararen hula.

Tun a shekarar 2013 ne masu shigar da ƙara na Birtaniya suka fara ƙoƙarin ƙwace ƙadarorin Ibori, amma aka yi ta cin karo da tarnaƙi da ɓata lokaci daga kotunan Landan.

A watan Yuli, alkali ya bayar da umarnin ƙwace fan miliyan 101.5 ($123.9 million) daga wajensa, ɗaya daga cikin manyan hukuncin da aka yanke a ƙarƙashin dokar Birtaniya ta aikata miyagun laifuka tun lokacin daka samar da ita a 2002.

Ya nemi umarnin a ba shi hutu don ɗaukaka ƙarar hukuncin, kuma a yanzu ana matakin farko-farko na ɗaukaka ƙarar.

Reuters