Daga Abdulwasiu Hassan
Nijeriya ta samu ‘yancin kai a ranar 1 ga watan Oktobar 1960 daga Birtaniya wadda ta yi wa kasashe da dama da ke Yammacin Afirka mulkin mallaka.
Daya daga cikin matakai mafi muhimmanci da kasar ta dauka shi ne yin kasa-kasa da tutar Birtaniya a ranar samun ‘yancin kai inda aka maye gurbinta da ta Nijeriya wadda Taiwo Akinwumi ya zayyana.
Tun bayan lokacin, Nijeriya ta rabu da abubuwa da dama na mulkin mallaka a yunkurinta na samun iko da kanta.
Ga wasu daga cikin abubuwan da Turawan Mulkin Mallaka suka bari wadanda Nijeriya ta yi watsi da su tsawon shekaru.
Taken Nijeriya
Taken Nijeriya wanda yake farawa da 'Nigeria We Hail Thee', ya kasance take ne wanda Nijeriya ta gada daga Birtaniya.
Wata Baturiya Lillian Jean Williams ce ta rubuta taken gabannin samun ‘yancin kai na Nijeriya.
An soma amfani da shi ne daga 1 ga watan Okotoba na 1960 zuwa 1978 a lokacin da aka fito da wani sabon taken kasar wanda har yanzu shi ake amfani da shi.
Sabon taken na Nijeriya an hada shi ne daga rubutun wasu fitattu biyar daga cikin gasar da aka saka ta rubuta sabon taken kasar.
Makadan ‘yan sandan Nijeriya ne suka mayar da shi wake karkashin jagorancin Benedict Odiase.
An hada wakar ne bayan an dauko kalamai daga rubuce-rubucen P. Aderibigbe da John Ilechukwu da Dakta Sota Omoigui da Emetim Akpan da B. Ogunnaike wadanda dukansu ‘yan Nijeriya ne.
Watsi da fam
Fam din Nijeriya ne kudin da ake amfani a lokacin da kasar ta samu ‘yancin kai.
Kudin wanda ya maye gurbin fam din Birtaniya na Yammacin Afirka an yi amfani da shi tun daga 1907 zuwa 1973 a lokacin da Nijeriya ta yanke shawarar samar da kudinta na kashin kai.
A lokacin ne Nijeriya ta samar da naira ₦ wanda har yazu ake amfani da ita.
Tukin mota
Tukin mota a Nijeriya ya kasance ana yinsa ne ta hannun hagu, wadanda motoci ne na Birtaniya da aka rinka shiga da su kasar.
An yi amfani da tsarin tukin motar na karin shekara 12 har zuwa lokacin da aka sauya zuwa hannun dama a 1972.
Kungiyar kwallon kafa
A lokacin samun ‘yancin kai, kungiyar kwallon kafa ta Nijeriya UK Tourist ana mata lakabi da “Red Devils” sakamakon jajayen kayan da suke sakawa.
Kungiyar ta buga wasa da sauran kasashe rainon Birtaniya tsawon shekaru kafin samun ‘yancin kai.
An sauya sunan kungiyar zuwa Green Eagles bayan samun ‘yancin kai inda aka sauya jajayen kayan zuwa tsanwa domin a samu daidaito da tutar Nijeriya.
Kungiyar ta samu sunanta na Super Eagles a 1988.
Tsarin Majalisa
Nijeriya ta gaji tsarin Majalisar Ingila bayan samun ‘yancin kai. Sir Abubakar Tafawa Balewa shi ne ya kasance Firaiminista inda Nnamdi Azikiwe ya kasance shugaban kasa.
Zauren majalisa daya kasar ke da shi a lokacin.
An daina amfani da tsarin bayan juyin mulkin farko da aka yi a Nijeriya a 1966.
Kasar ta ci gaba da zama a karkashin mulkin soji har zuwa 1979 a lokacin da aka mayar da mulki hannun gwamnatin dimokuradiya inda aka samar da tsarin mulkin shugaban kasa wanda ake da shi a yanzu.
Babu ofishin firaiminista, karfin iko na hannun shugaban kasa sai kuma majalisa ta rabu gida biyu – Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai.
Tsarin yanki-yanki
A lokacin da Birtaniya ta bai wa Nijeriya ‘yancin kai a 1960, kasar wadda ke a Yammacin Afirka na da yankuna uku wadanda suka sa ta zama tarayya kamar yadda Turawan mulkin mallaka suka tsara.
Sai dai Nijeriya ta daina amfani da tsarin yanki-yanki inda aka samu sauyi matuka bayan shekaru inda aka soma yin jihohi 12 wadanda suka maye gurbin yankunan kasar a 1967.
Bayan nan sai aka kara yin wasu jihohi a yayin da ake samun ci gaba a siyasar Nijeriya har aka samu jihohi 36.
Jihohin su ne masu iko na biyu bayan gwamnatin tarayya karkashin ikon shugaban kasa sa’annan sai kananan hukumomi.
‘Yan sanda
A lokacin samun ‘yancin kai, inifam din ‘yan sandan Nijeriya sun kasance ruwan toka da tsanwa inda maza ke saka gajeren wando.
Sai dai an sauya launin inifam din zuwa baki a 1988 inda aka bari duka jami’an ‘yan sanda su rinka saka dogayen wando a maimakon guntaye.
Duk da cewa daga baya an kawo wa ‘yan sandan shudin inifam, amma duk da haka ana amfani da bakaken.
Legas zuwa Abuja
Legas ta kasance babban birnin Nijeriya kuma babban birnin kasuwanci tun zamanin mulkin mallaka.
Sai dai bayan an dauki shekaru ana tsare-tsare da sauye-sauye, an mayar da babban birnin Nijeriya zuwa Abuja a Disambar 1991.
Wannan na daga cikin manyan sauye-sauyen da aka gudanar a Nijeriya bayan samun ‘yancin kai a 1960.
Legas ta kasance babban birnin kasuwancin kasar har zuwa yanzu. An mayar da ofishin shugaban kasa da majalisar kasar da ma’aikatun gwamnati zuwa babban birnin kasar wanda yake a tsakiyar kasar.
Haka kuma ofisoshin jakadanci su ma sun mayar da ofisoshinsu Abuja daga Legas.
Tsarin Ilimi
Zuwa lokacin da aka samu ‘yancin kai, tsarin ilimi a Nijeriya ya kasance kamar irin na Birtaniya, inda ake shekara shida a firamare, sai shekara biyar a sakandare sai shekara biyu na matakin A Level.
Nijeriya ta yi watsi da wannan tsarin a 1973 inda ta mayar da shi 6-3-3-4, wanda hakan ke nufin za a yi shekara shida a firamare sai uku a karamar sakandare sai uku a babbar sakandare sai shekara hudu a jami’a.
Makarantar soji
Babbar makarantar da ake ake horar da sojoji a Nijeriya a baya ana kiranta Royal Military Forces Training College RMFTC wadda sojojin Birtaniya ke gudanar da ita.
Sai dai an mayar da ita Nigerian Training College bayan samun ‘yancin kai.
A 1964, an sake sauya sunan zuwa Nigerian Defence Academy wanda har yanzu sunan ake amfani da shi.
A NDA ne ake horar da sojojin Nijeriya tun daga sojin kasa da na ruwa da na sama.
Duk da cewa Nijeriya ta gudanar da sauye-sauye da dama ta bangaren siyasa zamantakewa da tattalin arziki tun daga samun ‘yancin kai a 1960 tare da watsi da wadanda ta gada daga Turawan mulkin mallaka, har yanzu kasar na da kyakkyawar alaka da Birtaniya.
Nijeriya na daga cikin manyan kasashen Kungiyar Rainon Ingila haka kuma Ingilishi ne harshen da kasar ke amfani da shi na bai daya domin magana a kasar.