Shugabannin Nijar da Mali da Burkina Faso a birnin Yamai na Nijar ranar 6 ga watan Yuli 2024. / Hoto: Reuters

Ƙungiyar Sahel Alliance ta ƙasashen Burkina Faso, Mali da Nijar ta sanar da cewa fasfon ƙungiyar zai soma aiki 29 ga Janairun 2025.

Shugaban ƙungiyar ta AES Assimi Goita ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis 23 ga Janairun 2025 a wata sanarwa ta musamman.

Sanarwar ta ce duk da cewa sabon fasfon zai fara aiki daga 29 ga Janairun 2025, masu tsohon fasfo wanda ke da tambarin ECOWAS na da zaɓin su ci gaba da amfani da fasfon su har zuwa lokacin da wa’adinsa zai ƙare ko kuma za su iya zuwa a sauya musu sabon fasfo mai ɗauke da tambarin AES.

“A wani ɓangare na aiwatar da manufofi, musamman abubuwan da suka shafi zirga-zirgar 'yan kasa ba tare da tsaiko ba, shugaban kungiyar ta Sahel Alliance (AES) na sanar da kungiyoyin tarayya da na kasa da kasa game da fara aikin fasfo na AES, daga ranar 29 ga Janairu, 2025,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

“Haka kuma ‘yan ƙasashen ƙungiyar AES waɗanda suke riƙe da tsohon fasfo da ke da tambarin ECOWAS waɗanda wa’adinsu bai ƙare ba za su iya zuwa a sauya musu sabo da tambarin AES kamar yadda dokoki suka tanada,” kamar yadda sanarwar ta ƙara da cewa.

TRT Afrika