Kwamitin karbar mulki na zababben gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da aka fi sani da Abba Gida-Gida, ya yi korafi kan yadda gwamnatin jihar mai barin gado ta ki ba shi hadin kai don tsara yadda za a karbi mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
A wani taron manema labarai da kwamitin ya gudanar ranar Juma’a, shugabansa Dr Abdullahi Baffa Bichi ya koka kan abin da ya kira jan kafa da bangaren gwamnati ke yi don gudanar da shirye-shiryen mika mulki.
Dr Bichi ya ce kwanaki kadan bayan kafa kwamitin ne suka aika wa gwamnatin jihar takardar neman su fara zama tare don tsara komai, “amma sai kwamitin gwamnatin ya aiko mana amsa cewa mu bayar da mutum uku a matsayin wakilai da za su zauna da nasu kwamitin don yin hakan.”
“Mu kuma muka ga kamar gwamnati ba ta fahimci abin da ake so a cimma ba, bangarori ne biyu tsakanin mu da su don haka ba yadda za a ce za mu yi aiki karkashin kwamiti daya,” in ji Dr Bichi.
TRT Afrika ta tuntubi kwamishinan yada labarai na Jihar Kano Malam Muhammad Garba, wanda ya ce ba zagon kasa gwamnatinsu take yi wa gwamnati mai jiran gado ba.
“An bukaci su bayar da mutum ukun ne don a fara tattauna yadda al’amuran za su gudana ba wai don a fara sa hannu kan rahotannin da kwamitocin za su sa hannu a kai ba,” in ji shi.
An yi zaben gwamnan Jihar Kanon ne a ranar Asabar 18 ga watan Maris, inda a ranar Litinin 20 ga Maris aka sanar da Abba Gida-Gida a matsayin wanda ya yi nasara da kuri’a sama da miliyan daya, ya bai wa abokin takararsa na jam’iyya mai ci Nasiru Yusuf Gawuna tazarar kuri’a sama da 130,000.
Kwana biyu bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya INEC ta mika wa Injiniya Abba takardar shaidar lashe zabe ne sai ya kafa kwamitin karbar mulki mai mambobi 65, karkashin jagorancin Dr Baffa Bichi.
“Abba ya bayyana kudurori da ayyukan da kwamitin zai yi wajen taimakawa don a samu musayar gwamnati cikin jin dadi da lumana da abin da sabuwar gwamnati za ta yi idan ta kafu,” in ji shugaban kwamiitn.
Ya kuma tabbatar da cewa ita ma gwamnati mai barin gado ta kafa kwamiti mai mutum 17.
Ainihin korafin kwamitin Abba Kabir
Dr Bichi ya ce bayan haka ne kwamitinsu ya aika wa bangaren gwamnati mai barin gado takarda ta neman su zauna don fara aiki tare.
“Sai gwamnati ta aiko da amsa cewa mu bayar da mutum uku da za su yi aiki da kwamitin gwamnati, sai muka ga kamar gwamnati ba ta fahimci abin da ake so a cimma ba.
“Ba zai yiwu mu yi aiki karkashin kwamiti daya ba tun da alkiblar kowa daban, shirinsu daban kuma aikin mai karbar mulki daban da na mai ba da mulki,” in shi shi.
Dr Bichi ya ci gaba da cewa “Mun yi kokarin jawo hankalinsu cewa tsarin karbar mulki na zuwa da salo kala uku.
“Akwai yanayin da gwamnati mai ci ita ce aka sake zaba za ta ci gaba, wato gwamna zai yi tazarce, a irin wannan yanayi babu batun samar da kwamitin karbar mulki.
“Akwai yanayin da sabuwar gwamnati da gwamnati mai ci duk jam’iyyarsu daya, akida da alkiblarsu daya, to a irin wannan yanayi za a iya yin kwamitin karbar mulki daya.
“Sannan akwai irin na yanayinmu gwamnati mai tafiya da mai zuwa jam’iyyunsu daban, alkiblunsu daban don haka kowa zai kafa kwamitinsa,” ya jaddada.
Ya ce bayan shafe karin kwanaki sai aka aiko musu da takarda daga bangaren gwamnati cewa ana musu tunin aika sunan mutum uku da za a sa a kwamitin.
“Muka sake nanata musu cewa so muke kwamitinsu da namu su zauna tare don fayyace yadda abubuwa na karbar mulki da ranar rantsuwa za su kasance.
“Amma sai suka sake nuna mana cewa gwamna bai ma kaddamar da kwamitinsu ba don haka ba za su iya yin komai tare da mu ba sai gwamna ya kaddamar da nasu.”
Ya ba da misalai kan yadda aka dinga bin tsarin kafa kwamitocin karbar mulki a 2003 tsakanin Injiniya Rabi’u Kwankwaso da Malam Ibrahim Shekarau da 2011 tsakanin Shekarau din dai da Kwankwaso da kuma na 2015 tsakanin Kwankwaso da Abdullahi Umar Ganduje.
“Amma yanzu sati hudu da kafa namu kwamitin amma gwamna ya gaza kaddamar da kwamitin bangaren gwamnati,” Dr Bichi ya koka.
Daga nan shugaban kwamitin gwamnati mai jiran gadon ya yi kira ga Gwamna Ganduje da “ya dubi baiwar da Allah Ya yi masa da karamcin da jama’ar Kano suka masa ya daina kokarin kawo tarnaki ga kafuwar sabuwar gwamnati.”
Daukar mataki
Kwamitin Injiniya Abba Yusuf ya ce ba za su ci gaba da jiran bangaren gwamnati ba don haka akwai matakan da za su fara kaddamarwa daga ranar Litinin mai zuwa.
“Mataki na farko za mu kira taron tattaunawa da duk sakatarorin dindindin na ma’aikatu na wannan jihar ranar Talata 2 ga Mayu.
“Abu na biyu za mu sa kananan kwamitioci 33 na babban kwamiti su fara ganawa da tattaunawa da dukkan shugabannin ma’aikatun gwamnati, za a sanar da rana nan gaba.
“Za mu gana da shugaban ma’aikatan kananan hukumomi 44, za a sanar da rana nan gaba,” kamar yadda ya bayyana. Dr Bichi ya ce dalilin ganawar da su shi ne don lokaci na tafiya na rantsar da sabon gwamna.
Ya ce suna kuma sa ran karbar takardun mika mulki daga hannun gwamnati mai tafiya don fitar wa da sabon gwamna komai filla-filla don sanin ina aka tsaya kuma ina za a dora. “Za a yi hakan ne don tabbatar da cimma nasara.
“Mun so a yi wannan aiki da kwamitin gwamnati amma tun da gwamna ya ki ba da hadin kai shi ya sa muka dauki aniyar yin aikin tare da ma’aikatan gwamnati na dindindin don sanin halin da muke ciki.”
Shugaban kwamitin ya kuma tabbatar da karbar mulki “cikin mutunci da lalama don ci gaban Jihar Kano.”
Cikakken martanin gwamnatin Jihar Kano
Kwamishina Muhammad Garba ya ce ba dole sai gwamna ya kaddamar da kwamiti sannan za a zauna ba da dayan kwamitin ba.
“Kuma mutum ukun da muka bukaci su kawo su hadu da namu mambobin don a fara tsara yadda zaman kwamitocin biyu za su kasance ne,” ya ce.
Malam Garba ya ce suna da kwamiti na ma’aikatu da hukumomin gwamnati kuma “ba magana ce ta ba a so a yi aiki da su ba, wasu jihohi ma irin su Filato duk haka suke yi.
Kan batun matakan da bangaren Abba Kabir ya dauka na ganawa da shugabannin hukumomin wamnati da sakatarori kuwa, kwamishinan ya ce ba abin da zai ce don ba huruminsa ba ne.
“Idan sun ga abin da ya dace ne to wannan su da gwamnati ne. Mun sha fada cewa a daina hanzari, a tsaya a bi tsari kamar yadda kowace jiha take yi, amma mu ana ta samun rudani.
“Duk bayanan da suke nema za su same su a kundin bayanan mika mulki. Ya danganta da lokacin da aka kammala hada kundin sai a ba su don gwamna ya sa hannu su ma Bichi su saka hannu.”
Sai dai duk da haka kwamishinan ya tabbatar da cewa a karshe dai dole a samu lokaci da kwamitocin za su zauna bayan ma’aikatu sun aiko da rahotannin komai.