A ranar 29 ga watan Mayu aka rantsar da Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan Jihar Kano. Hoto/Abba Kabir Yusuf

Gwamnan Kano da ke arewacin Nijeriya Abba Kabir Yusuf ya mika wa majalisar dokokin jihar sunayen mutum 19 wadanda yake son nadawa kwamishinoni.

Wani jami’in gwamnatin Kano, wanda ba ya so a ambaci sunansa, ya tabbatar wa TRT Afrika cewa ana sa ran nan ba da dadewa ba majalisar jihar Kano za ta karanta sunayen a zaurenta sannan a gayyace su domin tantancewa.

Mutum goma sha taran da aka aika da su sun hada da:

- Kwamared Aminu Abdulsalam

- Honarabul Umar Haruna Doguwa

- Honarabul Ali Haruna Makoda

- Honarabul Abubakar Labaran Yusuf

- Honarabul Danjuma Mahmoud

- Honarabul Musa Shanono

- Honarabul Abbas Sani Abbas

- Hajiya Sani Saji

- Dakta Ladidi Garko

- Dakta Marwan Ahmad

- Injiniya Muhammad Diggol

- Honarabul Adamu Aliyu Kibiya

- Dakta Yusuf Kofar Mata

- Honarabul Hamza Safiyanu

- Honarabul Tajo Usman Zaura

- Sheikh Tijjani Auwal

- Honarabul Nasir Sule Garo

- Honarabul Haruna Isah Dederi

- Honarabul Baba Halilu Dantiye

A tsarin doka, sai majalisa ta kira mutanen da gwamnan ya zaba ta tantance su kafin a tabbatar da su a matsayin kwamishinoni.

Majalisar na da ikon kin amincewa da wani ko wasu da take ganin ba su cancanta ba ko kuma ba ta gamsu da su ba domin rike mukamin.

TRT Afrika