Kudancin Maroko ya jima yana fuskantar ruwan sama mai ƙarfi a 'yan kwanakin nan. / Hoto: AP

Akalla mutane takwas ne suka mutu yayin da wasu 15 suka ɓace sakamakon ambaliyar ruwa a kudu maso gabashin Maroko, kamar yadda hukumomi suka sanar a ranar Lahadi.

"An gano gawarwakin mutum takwas, yayin da wasu 15 suka ɓace a ambaliyar da ta yi sanadin rugujewar gidaje da dama a birnin Tata," in ji Omar Bahoush, magajin yankin Tamanart, a tattaunawarsa da gidan talabijin na Channel 2 na yankin.

Ambaliyar ruwan wadda ta afku da yammacin ranar Asabar, ta yi barna sosai a yankin, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka bayyana.

A ranar Juma'a babban daraktan kula da yanayi na kasar Maroko ya yi gargadi game da ruwan sama mai tsawon milimita 150 a yankuna da dama na kasar da ke arewacin Afirka.

Ambaliyar ruwa

Bahoush ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa ambaliyar ta lmamaye tituna tare da lalata hanyoyin sadarwa a birnin, wanda hakan ya kawo cikas wurin gano ainahin adadin mutanen da suka ɓace.

Kudancin Maroko dai ya jima yana fuskantar ruwan sama kamar da bakin kwarya a cikin 'yan kwanakin nan, wanda ya sake cika madatsun ruwa na ƙasar waɗanda suka jima suna fuskantar ƙarancin ruwan sakamakon raguwar da aka samu na ruwa a 'yan shekarun nan.

Sai dai wannan ruwan ya jawo barazana matuƙa ga ɓangaren noma na ƙasar.

Ko a ranar Laraba sai da mutum uku suka rasu sakamakon ambaliyar da ta shafe wasu birane a gabashin Maroko sakamakon mamakon ruwan sama.

AA