Fursunoni da dama ne suka tsere daga babban gidan yari da ke wajen Monrovina babban birnin Liberia a ƙarshen makon da ya gabata, in ji mahukunta a ranar Litinin.
Fursunonin 47 sun tsere ne saboda taɓarɓarewar tsaro a gidan kurkukun, in ji wata sanarwa da Ma'aikatar Shari'a ta fitar.
Kurkukun na garin Kakata mai nisan kilomita 55 arewa maso-gabas da babban birnin Monrovia.
Ma'aikatar ta kuma ce sun "damu matuka game da wannan lamari, kuma suna ɗaukar dukkan matakan da suka dace na tabbatar da sake kamo fursunonin da suka tsere."
An kara yawan 'yan sanda masu bincike
Rundunar 'yan sanda ta Liberia ta bayyana kara yawan jami'ai don aikin nemo fursunonin da suka tsere, in ji ma'aikatar.
Gidajen kurkuku a Liberia na cike da jama'a, inda fursunoni ke rasa isasshen abinci da magungunan kula da lafiya.
A shekarar da ta gabata, kayan abinci sun kare a gidan kurkuku da ke Monrovia, inda wasu gidajen kurkukun kasar ma suka daina karbar fursunoni saboda karancin abinci.
Ana kuma tsare da fursunoni da dama ba tare da yi musu shari'a ba. A watan Nuwamban 2022, wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya gano cewa kashi 73 na fursunonin da ke daure a gidajen kurkukun Liberia na zaman jiran a yanke musu hukunci ne.