'Yan takarar biyu Boakai da Weah ba su yi nasarar samun kashi 50 cikin 100 na kuri'u ba a zagayen farko na zaben da aka gudanar a watan jiya/ Hoto: Getty Images

'Yan kasar Laberiya za su sake fita rumfunan zabe don kada kuri'a ranar Talata a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar tsakanin Shugaba George Weah da tsohon mataimakin shugaban kasar Joseph Boakai, bayan fafatawar da aka yi a zagayen farko ba a samu wanda samu kashi 50 cikin 100 na kuri'un da aka jefa ba.

Tsohon dan wasan kwallon kafa Weah ya samu kashi 43 .83 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zagayen farko yayin da Boakai ya ci kashi 43.44.

Sakamakon 'yar karamar ratar da aka samu tsakanin 'yan takarar biyu da kuma rashin samun dan takara na uku mai karfi da ya biyo bayansu, na nufin za a sake fafatawa sosai a zagaye na biyu na zabe, a cewar wata kwararriyar mai sharhi kan bututuwan da suka shafi nahiyar Afirka Maja Bovcon wacce ke aiki da kamfanin leken asiri Verisk Maplecroft.

"Sauran kuri'un da suka rage a zagayen farkon sun rabu ne tsakanin ' yan takara 18 wadanda a yanzu suka fita daga cikin zaben. 'Yan takara biyu da za su fafata a zabe mai zuwa suna bukatar goyon bayan 'yan takarar da suka sha kashi a zagaye na farko," in ji Bovcon.

Zaben zagaye na biyu zai zama maimaici irin wanda aka yi a shekarar 2017 inda Weah ya samun goyon bayan jama'a da ya kai shi ga doke Baokai da kashi 61.54 cikin 100 na kuri'un da aka kada.

Daidaitawa

Weah ya yi nasara bisa alkawarin magance matsalar cin-hanci da rashawa da inganta rayuwa a kasar wacce ke yankin yammacin Afirka da ke kokarin farfadowa daga yakin basasa guda biyu da aka yi tsakanin shekarar 1989 zuwa 2003 da kuma annobar Ebola da ta yi sanadin mutuwar dubban mutane daga 2013 zuwa 2016 a kasar.

Sai dai wasu masu kada kuri'a sun nuna rashin gamsuwa game da yadda Weah ke gudanar da ayyukansa, musamman kan yaki da cin-hanci da rashawa da rashin ayyukan yi da matasa ke fuskanta da hauhawar farashin kayayyaki da kuma matsalar tattalin arziki gaba daya.

Ya kori shugaban ma'aikatan fadarsa da wasu manyan jami’ai biyu bayan da Amurka ta kakaba musu takunkumi kan cin hanci da rashawa.

Weah ya dora alhakin rashin cim ma manufofin tattalin arzikin kasar kan bullar cutar korona da kuma sakamakon yakin Rasha da Ukraine.

Gabanin zaben zagaye na biyu, 'yan takarar biyu sun samu amincewa daga 'yan takarar da suka sha kaye a zagayen farko.

Weah ya samu goyon bayan jam'iyyar CCP ta Alexander Cummings.

Tashin hankali

"Na zabi Cummings a zaben da ya gabata amma a wannan karon, George Weah zan bai wa kuri'a ta," in ji Martin Sumo, wani mai goyon bayan Cummings.

Boakai ya samu goyon baya daga 'yan takara uku a cikin hudu da suka sha kaye a zagayen farko na zaben.

Mai sharhi kan harkokin siyasa Bovcon ta ce duk da adadin goyon bayan da Boakai ya samu zai yi wahala ya samu kashi 50 da ake bukata don samun nasara a zaben.

Sai dai wani abu da za a iya mayar da hankali a kai shi ne kashi kusan 6 cikin 100 na kuri'un da aka soke a zagayen farko.

Edward Appleton Jr, wanda ya zo na uku a zagayen farko na zaben da kashi 2.20 cikin 10 na kuri'un da aka kada, ya ba da goyon bayansa ga Boakai a ranar Talata, yana mai cewa ''Yan Liberiya suna bukatar shugabanci da zai samar wa kasar sakamako mai kyau."

An dai gudanar da zagayen farko na zaben cikin lumana duk da cewa an samu tashe-tashen hankula a wasu wuraren sannan an kashe mutane biyu a rikicin da ya shafi zabe.

Bovcon ta ce akwai yiwuwar a fuskanci tashin hankali a zagaye na biyu.

“A fafutukar da suke yi na tabbatar da sun samu kuri’u, ‘yan takarar biyu za su iya haifar da rarrabuwar kawuna ko kuma hargitsi, kuma yin hakan na iya janyo tarzoma a kan tituna,” in ji ta.

TRT Afrika