Matsalolin da Liberiya ta shiga a lokacin yakin basasa da kuma rashin tabbas kan siyasar kasar a daidai lokacin da kasar ke tunkarar zabe a ranar 10 ga watan Oktoba domin zaben shugaban kasa da sanatoci 15 da ‘yan majalisar wakilai 73.
Zabe na da matukar amfani ga wannan kasar da ke Yammacin Afirka a daidai lokacin da kasar ke fama da matsin tattalin arziki da kuma kokarin cire miliyoyin ‘yan kasar daga talauci.
Amma ga masu sa ido da dama wadanda ke cikin damuwa, akwai alamu da ke nuna cewa za a iya samun rikici a lokacin zabe.
“Mun damu da rahotannin da aka ruwaito na tashe-tashen hankula da suka shafi zabe, wadanda za su iya kaiwa ga kalaman kiyayya, da kuma hare-haren da ake kai wa 'yan jarida a Liberiya gabanin babban zaben da za a yi a ranar 10 ga Oktoba," in ji Majalisar Dinkin Duniya a shafinta na intanet, kwanaki kafin zaben.
Seif Magango wanda shi ne mai magana da yawun Hukumar Kare Hakkin Bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana a Liberiya, wannan damuwar ta samo asali ne daga arangamar da aka yi tsakanin magoya bayan jam’iyyar adawa ta Unity Party da kuma jam’iyya mai mulki ta Coalition for Democratic Change a Satumba.
Akalla mutum biyu suka rasu, kuma mutum 20 aka raunata a Foya da ke Lofa da ke Arewacin Liberiya.
Guguwar sauyi
Shugaba George Weah, wanda tsohon dan kwallon duniya ne, na neman wa’adi na biyu a karkashin Jam’iyyar Coalition for Democratic Change inda ya kara jaddada alkawarin da ya yi ga kasar a lokacin da aka zabe shi a 2017.
Weah ya samu nasara a zabensa na farko na shugaban kasa a zagaye na biyu inda ya samu kaso 61.5 na kuri’u, inda ya doke Joseph Boakai na Jam’iyyar Unity.
Tun bayan da aka zabe shi, ya sha caccaka daga mutanen da ke cewa har yanzu Liberiya na gwagwarmaya. Shirin Ci-Gaba na Majalisar Dinkin Duniya ya ce mutanen da ke cikin talauci a Liberiya sun wuce kaso 52.3 cikin 100.
Weah ya yi kokarin yaki da cin hanci da rashawa a cikin gwamnatinsa inda har Amurka ta saka takunkumi kan wasu jami'an gwamnatinsa uku, daga ciki har da shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin na kasar Nathaniel McGill kan zargin almundahana da kudin kasa. Weah ya kori wadannan jami'an duk da sun musanta hakan.
A 2018, wata kotu a Liberiya ta bayar da sammaci ga sama da mutum 30 wadanda tsofaffin ma'aikatan babban bankin kasar ne kan zargin almundahana ta sama da dala miliyan 104 na kudin al'umma.
‘Yan takara da dama
Weah na fafatawa da ‘yan takara 19 a wannan karon, daga ciki har da Alexander Cummings wanda wani dan kasuwa ne, sai Taiwan Gongloe wanda lauyan kare hakkin bil adama ne, da kuma Joseph Boakai na Jam’iyyar Unity Party wanda shi ne babban dan adawa.
Sai dai a sakamakon kasar wadda ke da rabuwar kan jam’iyyu, fargabar da ake ciki ta zuwa zabe na kokarin komawa tarzoma.
“An sha samun barkewar rikicin zabe a Nimba da Montserrado da yankunan Grand Cape, inda har aka kai hari kan ‘yan jarida takwas, inda aka raunata biyu,” kamar yadda aka bayyana a shafin Majalisar Dinkin Duniya.
Kris Kieh, wanda dan jarida ne na Liberiya, na ganin akwai rashin tabbas dangane da halin da ake ciki. “An kai hari kan ‘yan jarida sakamakon suna tunanin muna amfani da aikinmu domin caccakar aikinsu,” kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
“’Ana kai hari kan ‘yan jarida masu zaman kansu musamman saboda irin labaran da suke bayarwa marasa dadi, wadanda ‘yan siyasa ke ganin makami ne na lalata su. Suna yin duk mai yiwuwa domin saka mu yin shiru.”
Damuwar jama’a
Damuwa tsakanin ‘yan jarida na kara bazuwa musamman wadanda suke rahototanni kan zabe, inda talakawan Liberiya ke jira su ji me za su ce a labarai.
“Ta ya za ku yi magana kan ci gaban tattalin arziki ga shi kuma ba ku da zaman lafiya?” in ji Sam Goncolo mazaunin Monrovian. “Wannan shi ne kawai abin da nake bukata daga gwamnati, mai tafiya da mai zuwa.
Ba za mu iya aiki mu samu arziki a matsayinmu na kasa idan babu zaman lafiya, duk da bambancin siyasa,” kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
A bangaren nasu, Shugaba George Weah, da kuma kuma babban abokin adawarsa Joseph Boaka, sun yi Allah-wadai da rikicin da ake yi, inda suka yi tuni ga magoya baya a wuraren yakin neman zabe cewa babu wani dalili a shari’ance na tayar da tarzoma a duk halin da ake ciki.
Alkawuran yakin neman zabe
Yaƙin neman zaɓen Weah ya ta'allaka ne kan samun daidaituwar tattalin arziki a Liberiya duk kuwa da matsalolin da ake fuskanta daga yaƙin da ake yi a Ukraine, da hauhawar farashin kayayyaki, da kuma karin bukatu daga kasashen da suka ci gaba a cewar Bankin Duniya.
Hakar ma’adinai da noma su ne suka kan gaba, inda aka samu ci gaba da kaso 5.9 cikin 100 daga 3.3 a 2021 sakamakon karuwa ta fannin noman shinkafa da rogo.
Sai dai Boaka na ganin har yanzu ba a ga wannan ci gaban ba a fili sakamakon mutanen karkara ba su shaida ba.
Ya ce idan aka zabe shi, ya yi alkawarin samar da sauye-sauye ga manoma wadanda za a shaida a kwanaki 100 bayan hawansa karagar mulki.
Hukumar zaben Liberiya ta tantance jam’iyyu 46 gabannin zaben, inda aka yi wa sama da mutum miliyan 2.4 rajistar zabe.