Tsakiyar yankin Sahel yana fuskantar ɗaya daga cikin gagaruman sauyi masu tasiri biyo bayan ficewar ƙasashen Burkina Faso da Nijar da Mali daga ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Yammacin Afirka ECOWAS da kuma kafa ƙungiyar ƙasashen Yankin Sahel (AES).
Abin da ya fara kamar jerin tashe-tashen hankula na soji a Mali da Burkina Faso da Nijar ya koma wani sauyi na tsarin tsaro da haɗin kai na hukumomi da kuma tasiri na ƙetare da ke kawo ƙasashe maƙwabta irin su Aljeriya da Maroko da ƙasashe masu ƙarfi cikin gogayya.
Kawo yanzu dai AES ta ƙarfafa kanta a matsayin wata kafa ta siyasa da tsaro da ta sha bamban da ƙungiyar ECOWAS. Da gangan Aljeriya ta bar batun matsalar diflomasiyya zuwa alaƙa ta yadda ta yiwu.
Gogayya ta yankin arewacin Afirka ta gangara kudu ta manufofi masu gogayya na ababen more rayuwa da haɗin kai. Ƙawancen waje yana faɗaɗa. Tare waɗannan ababen da suka faru suna samar da wani tsari na yanki mai iko da yawa wanda ya mayar da hankali kan ‘yancin kai kuma tasirinsa zai yi tasiri a kan tsarin tsaro na Yammacin Afirka nan da shekaru masu zuwa.
Ranar 9 ga watan Agusta na shekarar 2026, Aljeriya ta miƙa helikwaftan yaƙi biyu samfurin Mi-24V da kuma helikwaftan sufuri biyu samfurin Mi-171, tare da makamai da kayayyakin gyara da kuma tallafi na kaikomo ga Nijar.
Miƙa kayayyakin, a ƙarƙashin umarnin Shugaba Abdelmadjid Tebboune, an bayyana shi a Algiers ne a matsayin ƙarfafa alaƙa ta ‘yan’uwantaka da kuma wata gudumuwa ga zaman lafiayar yanki. A zahiri kuwa ta bayyana wani takamaimen abin da ya fi bayyana ta fannin soji na farfaɗo da alaƙa tsakanin Aljeriya da AES bayan ɓallewa da ta biyo bayan kakkaɓo jirgin saman Mali a watan Afrilun shekarar 2025 kusa da kan iyakar ƙasashen biyu.
Wannan lamarin ya haddasa janyewar jakadu daga manyan birane na ƙasashen AES uku da kuma ramuwar gayya ta taƙaita zirga-zirga a sararin samaniya. Daga farkon shekarar 2026 Algiers ta fara ja da baya ta hanyar dfilomasiyyar makamashi da ta ababen more rayuwa da tuntuɓar manyan shugabannin Nijar, da sake farfaɗo da tsare-tsaren kiyaye kan iyakoki da kuma dawo da dangataka ta diflomasiyya da sufurin sama da Mali.
Bayar da kyautar helikwafta ya cika jerin tallafi na tsaro ga ƙasashen AES a kan iyakar Sahel mafi girma.
Aljeriya ta nufi kudu — kuma Sahel ta buɗe ƙofa
Wannan wata hanya ce bayyananniya. Aljeriya ba ta dage kan sulhuntawa da dukkan ƙasashen AEs a lokaci ɗaya ba, kuma ba ta gindaya sharaɗin cewa sai sun koma tsarin ECOWAS ba kafin ta haɗa kai da su.
Ta ba da fifiko ga ƙawance da ya fi bada fa’ida ga ɓangarorin biyu da ƙarfafa tsaro a aikace da kuma haɗin kai na makamashi da amfani da kalamai masu ɗorewa na ‘yancin kai da rashin katsalandan kuma daga baya ne ta dawo da dangantaka da Bamako a ƙarƙashin matsi na taɓarɓarewar yanayin tsaro a arewacin Mali.
Dangantaka ta ƙasashe biyu ta kasance mai yiwuwa ko ma a lokacin da wasu tambayoyi na hukumomi suka kasance abin da ba a warware ba.
Wannan jerin aukuwar abubuwa wani ɓngare ne na tsari mai fitowa. Ƙungiyar AES ta kammala ficewarta daga ECOWAS, ta kafa wata rdununa ta haɗaka tare da faɗaɗa burin adadin dakaru, da kuma samar da tsare-tsare na diflomasiyya da na watsa labarai na daban.
Bayananta na siyasa sun mayar da hankali ne kan ‘yancin kai da watsi da abin da ake ganin tasiri ne na masu mulkin mallaka da kuma halaccin gwammnatoci na soji yayin da gyara ga gwamnatocin fararen hula da suka gaza biyan buƙata. Haɗa kai da Rasha da Aljeriya da sauran ƙasashen da ba na Yamma ba ne ana bayyana su a matsayin zaɓi na girmamawa da za su iya maye gurbin gwamnatoci na baya.
Kazalika gogayya a yankin Maghreb ya ƙara zafi. Manufar haɗakai na Aljeriya a yankin Sahara ta hanyoyi da wayar intanet da kuma ayyuka na bututun mai ta hanyar Nijar, a yanzu tana gogayya da tsarin kogin Atalantika na Maroko mai haɗa Nijeriya da tashoshin ruwan Maroko.
Gwamnatocin AES sun nuna iko na iya zaɓen abin da ya fi musu inda za su karɓi tallafi daga wani yanki yayin da suke barin wasu zaɓi a buɗe ga wasu zaɓin.
AES tana gini fiye da ECOWAS
Tasirin lamarin a yankin ya riga ya bayyana. Ga ECOWAS lamarin ya zurfafa raunin tsarinta. Rasa ƙasashen Sahel uku ya rage ƙarfi da faɗin ƙungiyar da kuma ƙarfinta kan rashin tsaro da ya fi shafar sauran mambobinta.
Tsare-tsaren tsaro na daban suna nan a halin yanzu tare da taƙaitaccen gurbin aiki. Ƙasashen da ke bakin teku sun ci gaba da tafiyar da yanayin barazanarsu yayin da ƙsashen Sahel suka mayar da hankali arewa domin neman zaɓi na daban da abokan aiki.
Ƙungiyar Tarayyar Afirka ita ce babbar ƙungiya ta nahiya wadda ke da ikon iya cike giɓin, duk da haka ƙarfinta na iya ƙaƙaba haɗin kai da tsaiko na tunanin ‘yancin kai da ya haddasa rarrabuwar kawuna.
Sakamakon tsaro dai kawo yanzu ya kasance a cakuɗe tsakanin nasara da rashin nasara. Tsare-tsare na kan iyaka da aka sake farfaɗowa da su da kuma miƙa taƙaitattun kayayyaki za su iya inganta dabaraun mayar da martani da kuma aikewa da gargaɗi da sauri a wasu kan iyakoki.
Sai dai ba sa magance matsalolin da ke haddasa tayar da ƙayar bayan irin su gazawar gwamnati da gogayya kan albarkatu da iko na iya sajewa na ƙungiyoyi irin su JNIM da ƙwayen ISWAP ba. Dangantaka ta ƙasashen biyu za ta iya ƙunsar wasu alamu, ba ta janyo zaman lafiya mai ɗorewa kai-tsaye ba.
A sabuwar gogayyar tasiri A Yammacin Afirka
A halin yanzu, shigar da hamayyar Aljeriya da Maroko cikin yankin Sahel shigowa da ƙarin rikicin siyasa cikin wani wuri da ya riga ya kasance mai sarƙaƙiya, duk da cewa ƙasashen AES da kansu suke fitar da fa’idoji daga gogayyar.
Nijeriya na da wata matsaya bayyananniya. Tana tarayya da Nijar a wasu jerin wurare na barazana kuma tafkin Chadi na bai wa Abuja wata bayyananniyar hanya ta aiki da Niamey. Duk da haka duk wani aiki dole ya bi ta kan muradun AES masu saɓawa aiki da ita wadda ta ke tayar da hankali kan alaƙa da Faransa ko kuma sharruɗan ECOWAS.
Saboda haka yanayin da ke fitowa yanzu wani yanayi ne da ba wai mai sauƙin komawa tsarin da ba ne kawai ko kuma cikakken rarrabuwar kai. Wani yanayi ne da ya ke da madafun iko da dama inda ƙasashen AES ke aiki da ƙarin iko, kuma gogayyar yankin Maghreb ke ci gaba da ƙarin abubuwan da za a iya smaarwa maimakon iƙirari na siyasa, kuma tasirin ECOWAS na raguwa, kuma dole masu aiki daga ƙetare su yi aiki a cikin wani wuri cike da bayanai na ‘yancin kai.
Ana ƙara auna tasiri ne bisa ikon iya samar da haɗin kai a aikace bisa ƙa’idoji da masu ryuwa da tsaki a suka aminta da shi.
Ko wannan sake fasalin abubuwan zai iya inaganta tafaiyar da tsaro ko kuma kawai sake rarraba ƙawance na etare za su dogara ne ga ingancin rarraba bayanan sirri daga baya, ɗorewar tsare-tsaren sabuwar danganataka da kuma niyyar dukkan ɓangarori su ba da fifiko ga tsarin rarrage barazana mai sauyawa bisa lamurra kan tagomashi na alabarai.
Ana sake taswirar Sahel ta hanyar tasirin mai ƙruwa na dangantaka a aikace na na ƙasashe da tarwatsa hukumomi da kuma tasiri na gogayya. Sakamakonsa zai wuce manyan biranen ƙasashen AES, inda zai tafiyar da tsarin tsaron Yammacin Afirka a gomman shekarun da ke tafe .
Marabucin, Dr. Kabir Adamu, shi ne manajan Daraktan , kamfanin Beacon Security and Innovations Limited, wani kamfanin da ke nazari kan tsaro a Abuja.
Togaciya: Ra’ayin da marubucin ya bayyana ba sa wakiltar ra’ayi ko manufofin TRT Afrika.

















