| Hausa
SIYASA
4 minti karatu
Martanin duniya a yayin da Isra’ila ke rajistar mallake Gabar Yammacin Kogin Jordan
Gwamnatin Isra’ila ta amince da wani kudiri na yin rajista a wasu yankuna da dama da ke Gabar Yamma a matsayin “Kadarorin Kasa”, wanda mataki ne da aka dauka karon a farko tun bayan mamaye yankin da Isra’ila ta yi a 1967.
Martanin duniya a yayin da Isra’ila ke rajistar mallake Gabar Yammacin Kogin Jordan
Falasdinawa na fuskantar hatsarin isa ga filaye da gonakinsu bayan kafa tutocin Isra'ila a ranar 15 ga Fabrairun 2026. / AA
16 Fabrairu 2026

Gwamnatin Isra'ila ta amince da wani tsari na yin rijistar filaye a Gabar Yamma da aka mamaye, wanda ya jawo suka daga kasashe daban-daban da masu suka wadanda suka kira shi "babban kwacen filaye" wanda zai hanzarta mamaye yankunan Falasdinawa.

Ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta ce matakin zai ba da damar "fayyace haƙƙoƙi da cikakken bayani game da warware takaddamar shari'a" kuma an buƙaci hakan bayan yin rajistar filaye ba bisa ƙa'ida ba a yankunan da Hukumar Falasdinawa ke iko da su.

Amma Turkiyya, Masar, Qatar da Jordan sun soki matakin a matsayin haramtacciyar doka a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa.

Ankara ta yi Allah wadai sosai da matakin na Isra'ila, tana mai cewa ya saba wa dokokin ƙasa da ƙasa.

A cikin wata sanarwa, ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya a ranar Lahadi ta bayyana cewa matakin yana nufin tilasta wa Isra'ila "ikon mallakar Gabar Yamma da aka mamaye da kuma faɗaɗa ayyukan matsugunan ‘yan kama wuri zauna"

"Wannan matakin, wanda ke neman tilasta wa al'ummar Falasdinawa da korar su daga yankunansu da kuma hanzarta yunkurin mamaya daga Isra'ila ba bisa ka'ida ba, ya nuna karara cewa an saba wa dokokin kasa da kasa kuma ba shi da amfani," in ji ma'aikatar.

Ma'aikatar ta kara da cewa, "Isra'ila ba ta da ikon mallakar yankunan Falasdinawa da aka mamaye," in ji ma'aikatar, tana mai cewa manufofin fadada yankunan da gwamnatin Firaminista Benjamin Netanyahu ke bi, na lalata kokarin zaman lafiya da kuma lalata damar samun mafita ta hanyar kafa kasashe biyu.

A ana cikin hakan, a cikin wata sanarwa, gwamnatin Masar ta kira matakin da "hatsarin da ke da nufin karfafa ikon Isra'ila kan yankunan Falasdinawa da aka mamaye".

Ma'aikatar harkokin wajen Qatar ta yi Allah wadai da "shawarar mayar da filayen Gabar Yamma zuwa abin da ake kira 'kadarorin kasa'," tana mai cewa zai "hana al'ummar Falasdinawa 'yancinsu".

Babban aikin kwace filaye da gonaki

Hukumar Falasdinawa ta yi kira shiga tsakanin kasa da kasa domin hana "farkon tsarin mamaye yankunan Falasdinawa da kuma rushe tushen kasar Falasdinawa".

Kungiyar adawa da Isra'ila mai fafutukar kare matsugunan Falasdinawa ta ‘Peace Now’ ta kira matakin na ranar Lahadi a matsayin "babban kwace filaye".

A cewar kafar watsa labarai ta gwamnati KAN, za a sake bude rajistar filaye a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye a karon farko tun shekarar 1967 - lokacin da Isra'ila ta mamaye yankin na Gabas ta Tsakiya.

Kafafen watsa labaran Isra'ila sun rawaito cewa tsarin zai gudana ne kawai a Yankin C, wanda ya kunshi kusan kashi 60 cikin 100 na yankin Gabar Yamma da aka mamaye kuma yana karkashin kulawar tsaro da gudanarwar Isra'ila.

Falasdinawa suna ganin Gabar Yamma da aka mamaye a matsayin ginshiki ga kowace kasar Falasdinu da za ta kasance a nan gaba, amma mutane da yawa da ke da ra'ayin addini na Isra'ila suna son kwace yankin.

A makon da ya gabata, majalisar tsaron Isra'ila ta amince da wasu matakai da ministoci 'yan ra'ayin mazan jiya suka goyi baya don ƙara tsaurara iko kan yankunan Gabar Yamma da Hukumar Falasdinawa ta mamaye karkashin yarjejeniyar Oslo da aka cim ma tun shekarun 1990.

Waɗannan matakan, waɗanda suka haifar da suka daga ƙasashen duniya, sun haɗa da barin 'yan Isra'ila Yahudawa su sayi filayen Gabar Yamma da aka mamaye kai tsaye da kuma ba wa hukumomin Isra'ila damar gudanar da wasu wuraren addini a yankunan da ke ƙarƙashin ikon Hukumar Falasdinawa.

Baya ga Gabashin Kudus da Isra'ila ta mamaye, sama da 'yan Isra'ila 500,000 suna zaune a matsugunai da wuraren da ke Gabar Yamma da aka mamaye, waɗanda haramtattu ne a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa.

Kimanin Falasdinawa miliyan uku ne ke zaune a yankin.

Rumbun Labarai
Trump ya bar ƙofar Iran a bude, kuma Netanyahu ba zai iya rufe ta ba
Yadda 'yan Nijeriya suka fusata kan matakin Amurka na saka wa Kwankwaso takunkumi
Majalisar Dattijan Nijeriya ta amince da tsarin aika sakamakon zabe kai-tsaye ta intanet
Taƙaddama a kan gyaran dokar zaɓe ta Nijeriya
Ghana ta yi wa jakadanta a Nijeriya kiranye kan zargin maguɗin zaɓe
Iran ta ce ta shiga tattaunawar Oman da Amurka da 'kyakkyawar niyya'
Masar da Saudiyya sun yi kira ga samar da hanyoyin da suka dace kafin tattaunawar Amurka da Iran
Greenland ba hajar sayarwa ba ce
Yayin da duniya ta koma kasuwar buƙatar diflomasiyya, wai zai tsaya wa ƙasashe marasa ƙarfi a 2026?
Amurka ta dakatar da bai wa ‘yan Nijeriya biza
Alkawarin dala miliyan 150 zai sake gina Aleppo da yaƙi ya lalata
Yadda 'nadamar zalunci' ke janyo rushewar lafiyar ƙwaƙwalwa a rundunar sojin Isra’ila
Me ya sa Trump da masu sharhi da ke da ra’ayin rikau ke sa ido kan al’ummar Somalia da ke Minnesota?
Shugaban Nijar Tiani ya karɓi shugaban Bilma bayan ya yi watanni 16 a hannun masu garkuwa da mutane
An daƙile harin RSF kan West Kordofan: Rundunar Sojin Sudan
Nijar ta ce ta fara kai uranium ɗinta kasuwar duniya
Trump ya ce Amurka za ta dakatar da hijirar 'yan cirani daga kasashe marasa arziki har abada
Gobarar Hong Kong: Adadin waɗanda suka mutu ya kai 128 yayin da aka shiga kwana uku a ƙoƙarin ceto
China ta yi gargaɗin 'murƙushe' katsalandan ɗin ƙetare kan shirin makami mai linzani na Japan
Yaƙin Sudan: Maye gurbin UAE da Turkiyya na iya ƙarfafa ƙoƙarin ƙasashe na samar da zaman lafiya