| Hausa
NIJERIYA
4 minti karatu
'Yanta'adda na Lakurawa sun kashe sojoji biyu da wani ɗan China a jihar Kebbi a Nijeriya
Sai dai kuma, dakaru sun samu sun daƙile wani hari kan wani sansanin soji a yankin daga baya inda suka ƙwace babura 17 da makamai.
'Yanta'adda na Lakurawa sun kashe sojoji biyu da wani ɗan China a jihar Kebbi a Nijeriya
Tsohon Hoto: Sojojin Nijeriya na yaƙar ta'addanci a sassan ƙasar

Wasu da ake zargi ‘yanta’addan Lakurawa ne sun kashe sojoji biyu da wani ɗan ƙasar China a harin da suka kai kan ma’aikatan gine-gine a Ƙaramar Hukumar Maiyama da ke jihar Kebbi a arewa maso yammacin Nijeriya.

Sai dai kuma, wasu dakarun tsaron ƙasar sun daƙile wani hari kan sansanin soji a yankin daga baya inda suka ƙwace babura 17 da makamai.

Hare-haren sun faru ne ranakun Laraba da Alhamis yayin da ‘yanta’addan masu yawa waɗanda rahaotanni suka ce suna kan babura fiye da 100, suka zafafa aika-aikarsu a yankin Maiyama, in ji majiyoyin tsaro.

Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan Nijeriya reshen jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya tabbatar da harin kan ma’aikatan gine-gine, yana mai cewa waɗanda lamarin ya rutsa da su suna cikin ma’aikatan da suke aikin gina babbar hanyar Sokoto zuwa Badagry ne a jihar.

Masu AlakaTRT Afrika - Ana zargin Lakurawa da kashe aƙalla mutum 28 a masallaci a Sokoto

Usman ya ce sojojin biyu suna ba da kariya ne ga ɗan ƙasar China ɗin da sauran ma’aikata a lokacin da ‘yanta’addan suka kai wani harin ba-zata.

Ya ce, “E, harin ya auku, amma ‘yanta’addan ba daga jihar Kebbi suke ba. Sun shigo jihar ne ta ɓarauniyar-hanya ta wani ƙauye da ke maƙwabtaka da jihar Kebbi.

“An kashe sojojin ne yayin da suke gadin ɗan China da sauran ma’aikata yayin da ‘yanta’addan suka kai wani hari na ba-zata, inda suka kashe sojoji biyu da wani ɗan ƙasar China tare da jikkata wasu,” in ji shi.

Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan ya ce ba zai iya bayyana sunayen sojojin da suka rasu ba saboda sojoji ne, ba ‘yansanda ba.

“Ba za mu iya ba ku sunayen waɗanda aka kashe a harin ba saboda su ba jami’an ‘yansanda ba ne,” a cewarsa.

Usman ya bayyana harin a matsayin “na jahilci da ba shi da dalili,” yana mai ƙarawa da cewa hukumomin tsaron sun ƙaddamar da aikin neman maharan.

Ya ce, “Tawagar haɗin gwiwa ta hukumomin tsaro ta fara neman waɗanda ake ganin ‘yanta’addan Lakurawan ne da suka kashe sojoji biyun da ɗan ƙasar China ɗaya.”

Sai dai kuma, Rundunar haɗin gwiwa ta Operation Fansan Yamma, ta daƙile wani harin wasu da ake zargin ‘yanta’addan Lakurawa ne kan sansanin sojin da ke Maiyama da sanyin safiyar ranar Laraba.

‘Yanta’addan, da rahotanni suka ce suna da yawa bisa babura da suka kai 100, sun danna sansanin sojin ne da makamai iri-iri, ciki har da bindiga mai jigida da gurneti da ake harbawa da roka.

Sai dai kuma, dakaru sun mayar da martani cikin gaggawa, inda suka tilasta wa maharan ja da baya daga yankin.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, jami’in watsa labaran rundunar haɗin gwiwar ta Operation Fansan Yamma, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya ce ‘yanta’addan sun bar makamansu da kayayyaki da sauran ababen guzurinsu yayin da suke tserewa.

Danja ya ce, “Dakarun sun mayar da martani cikin gaggawa kuma sun daƙile harin tare da hana ‘yanta’addan cim ma burinsu.”

Ya ƙara da cewa daga baya dakarun da suka ƙaddamar da aikin bin diddigin maharan a yankin sun samu babura 17 da wata bindiga mai jigida da wata bindiga samfurin AK-47 da sauran makamai da wata na’urar sadarwa.

Ya ce ababen da aka samu sun kasance wani babban koma-baya ga ikon aika-aikar ƙungiyar ‘yanta’addan a yankin.

“Samo makamai da harsashai da kayan sadarwa da babura alama ce ta babban koma-baya ga ikon aika-aikar ‘yanta’addan a yankin,” in ji shi.

Danja ya ce yankin na nan tsaf ƙarƙashin ikon dakarun, yana mai ƙarawa da cewa ana ci gaba da sintiri na nema da kuma kassara sauran mambobin ƙungiyar.

Ya ce rundunar Operation Fansan Yamma ta jajirce wajen kare al’ummomi da kuma hana ‘yanta’adda yin aika-aika a yankin.

Lamura na baya bayan nan ƙari ne ga damuwar tsaro a yankunan da ke tsakanin jihohin Kebbi da Sokoto masu maƙwabtaka, inda ake cewa waɗanda ake zargin ‘yanta’addan Lakurawa ne suna kai hare-hare da kuma kutsawa yankin.