Ministan Isra’ila mai tsaurin ra’ayi Itamar Ben-Gvir ya yada wani bidiyo yana nuna kansa yana hantarar wani dan gwagaarnaya mai goyon bayan Falasdinu, wanda aka durkusar ta karfi bayan sojojin Isra’ila sun yi garkuwa da su daga tekun kasa da kasa.
Kasashe goma da suka hada sa bakwai daga Turai sun aika sammace ga jakadun Isra’ila game da bidiyon da ya nuna abokin kawancen Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu kuma Ministan Tsaro Itamar Ben-Gvir na muzanta wani dan gwagwarnayar goyon bayan Falasdinawa da aka kama a jirgin ruwan Flotilla na Gaza.
Bidiyon na Ben-Gvir ya nuna shi yana hantarar ‘yan gwagwarnaya masu goyon bayan Falasdin, wanda aka durkusar ta karfi bayan sojojin Isra’ila sun yi garkuwa da su daga tekun kasa da kasa.
Ministan ya janyo harzuka daga ciki da sajen Isra’ila bayan yada bidiyon na minti guda.
Sojojin Isra’ila sun kai hari kan jirgin ruwan agajin a ranar Litinin a tekun kasa da kasa tare da kama dukkan mutanen da ke ciki. Jiragen na dauke da mutane 428 daga kasashen duniya 44, kuma sun bar tashar jiragen ruwa ta Marmaris da ke Turkiyya ranar Alhamis din makon jiya, da manufar kawar da kawanyar da Isra’ila ta yi wa Gaza tun 2007.
Italiya
Italiya ta aike da sammace ga jakadan Isra’ila a kasar don nuna bacin ranta game da abinda aka yi wa ayarin na ‘yan gwagwarnaya d ake hanyar zuwa Gaza inda ta nemi da a sako dukkan ‘yan kasarta da ake ci gaba da tsare wa, in ji Ma’aikatar Harkokin Waje. Sakatare Janar na Ma’aikatar Jakada Riccardo Guarigilia ya mika rashin jin dadin italiya ga jakadan Isra’ila.
Poland
Poland ta ce za a gayyaci mataimakin jakadan Isra’ila a Warsaw don neman sa da ya nemi gafara kan muzantawar da aka yi wa masu fafutukar da ke hanyar zuwa Gaza.
Ministan Harkokin Waje Radoslow Sikorski ya ce matakin na da manufar aike wa da bacin ran Warsaw game da mamban gwamnatin Isra’ila da ya aikata ba daidai ba.
Spaniya
Spaniya ta aike da sammace ga mataimakin jakadan Isra’ila bayan Ministan Harkokin Waje Jose Manuel Albares ya soki mummunan cin zarafin da aka yi wa ‘yan gwagwarnayar da aka kama.
A wani sakon bidiyo ta shafin X, Albares ya ce an ga yadda Ministan Isra’ila ya dinga muzanta ‘yan gwagwarnayar cikin rashin adalci da wulakantawa.
Faransa
Faransa ta aike da sammace ga jakadan Isra’ila don bayyana bacin ranta kan lamarin, in ji Ministan Harkokin Waje Jean-Noel Barrot. Ya kara da cewa Paris na neman ba’asi daga Isra’ila kan yadda aka mu’amalanci ‘yan gwagwarmayar.
Belgium
Belgium ta aike da sammace ga jakadan Isra’ila game da abin sosa rai da Ben-Gvir ya aikata wa ‘yan gwagwarmayar jirgin ruwan da ke zuwa Gaza wanda ‘ba za a amince da shi ba’, ta nemi da a sake su nan da nan.
Ministan Harkokin Waje Maxime Prevot ya ce bidiyon ya nuna ‘yan gwagwarmayar da aka kama, aka tilasta musu tsugunawa, yayin da ministan gwamnati ke yada wulakanta su a shafukan sada zumunta.
Holland
Holland ma ta shirya gayyatar jakadan Isra’ila a kasar game da mu’amala ‘mummuna da ba za a amince da ita ba’ da aka yi wa ‘yan gwagwarmayar da ke hanyar zuwa Gaza, in ji ma’aikatar harkokin waien kasar ranar Laraba.
Portugal
Ma’aikatar Harkokin Wajen Portugal ta yi suka da babbar murya kan muzantawar da Ben-Gvir ya yi wa masu fafutukar da ke cikin jiragen tuwa Sumud, tana mai cewa ta aike da sammace ga jakadan Isra’ila don mika masa korafi da neman karin haske, kamar yadda sanarwar ta bayyana a shafin X.
New Zealand
New Zealand ma ta shirya gayyatar jakadan Isra’ila game da bidiyon Ben-Gvir da yake Muzanta masu fafutukar da mahukuntan Isra’ila suka kama.
Ministan Barkokin Waje Peters ya ce tuni New Zealand ta kakaba takunkumin zuwa kasar ga Ben-Gvir tun shekarar bara saboda ‘hana samun zaman lafiya da gangan da yin zagon kasa ga shirin samar da kasashe biyu’.
Australia
An gayyaci jakadan Isra’ila a Australia zuwa Sashen Harkokin Waje da Kasuwanci don mika rashin jin dadin gwamnati game da bidiyon ministan tsaron kasa na Isra’ila yana wulakanta ‘yan gwagwarnayar da aka kama, in ji Ministan Harkokin Waje Penny Wong.
Kanada
Firaminista Mark Carney a ranar Laraba ya nuna rashin amincewa da mummunar mu’amala da aka yi wa ‘yan gwagwarmayar flotilla, yana mai neman Tel Avuv ta tabbatar da ‘lafiya da tsaron’ ‘yan kasar Kanada.
Da yake fadin Ma’aikatar Harkokin Wajen Kanada ta aike da sammace ga jakadan Isra’ila a Ottawa, Corney ta shafin X ya ce Kanada ta nemi a ba ta ‘tabbacin lafiya da tsaron ‘yan Kanada da ke cikin masu fafutukar’.












