| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Mutane 237 ne suka mutu sakamakon zazzaɓin Lassa a watanni bakwai na 2026 a Nijeriya - NCDC
Alƙaluman da ke ƙunshe a cikin Rahoton Yanayin Zazzaɓin Lassa na Hukumar NCDC, sun nuna ƙaruwar adadin kashi 23.7 cikin ɗari na waɗanda suka kamu da cutar.
Mutane 237 ne suka mutu sakamakon zazzaɓin Lassa a watanni bakwai na 2026 a Nijeriya - NCDC
Alkaluman, dake kunshe a cikin Rahoton Yanayin Zazzabin Lassa na NCDC, ya nuna ƙaruwar adadin wadanda suka kamu da cutar da kashi 23.7 cikin dari.

Aƙalla mutane 237 ne suka mutu a Nijeriya daga cikin 1,000 da aka tabbatar sun kamu da zazzaɓin Lassa a jihohi 23 da ƙananan hukumomi 116 a makonni 30 na shekarar 2026, a cewar Cibiyar Kula da Cututtuka masu yaɗuwa ta Nijeriya (NCDC).

Alƙaluman da ke ƙunshe a cikin Rahoton Yanayin Zazzaɓin Lassa na Hukumar NCDC, sun nuna ƙaruwar adadin kashi 23.7 cikin ɗari na waɗanda suka kamu da cutar.

A makon nazari kan cutar a ƙasar, an samu mutane 227 da ake zargi sun kamu da cutar, inda aka tabbatar da 17, sai kuma mutum shida da suka mutu, daga jihohin Ondo da Bauchi da kuma Benue.

Sabbin alƙaluman mutum 17 da aka tabbatar, sun nuna raguwa daga mutum 20 da aka ruwaito sun kamu da cutar a mako na 29 na ɓullar annobar a Nijeriya.

Ko da yake dai NCDC ta bayyana cewa adadin waɗanda ake zargi sun kamu da cutar tare da tabbatar sun kamu da cutar sun wuce adadin waɗanda aka tattara bayanansu a irin wannan lokaci a 2025.

A cewar rahoton, kashi 86 cikin 100 na wadanda aka tabbatar sun kamu da zazzabin Lassa a shekarar 2026 sun fito ne daga jihohi biyar da suka hada da Ondo da Bauchi da Taraba da Edo da kuma Benue.

Kazalika, kashi 32 cikin 100 na wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar sun fito ne daga jihar Ondo, sai kashi 25 cikin 100 daga Bauchi, yayin aka samu kashin 13 cikin 100 a Taraba, sai kashi 10 cikin 100 daga Edo, a Benue kuma an samu kashi shida cikin dari, yayin da sauran kashi 14 cikin 100 suka fito daga faɗin jihohi 18.

Cutar ta fi kama ‘yan shekaru tsakanin 21 zuwa 30, sai dai an samu rahoton kamuwar cutar daga mai shekara 1 zuwa 93 da matsakaicin shekaru na 30. Sannan alƙaluman mata da maza wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 1:0.9.

Kazalika NCDC ta bayyana cewa an samu wani ma’aikacin lafiya ɗaya da ya kamu da Zazzabin Lassa a makon da ake tattara bayanai, wanda hakan ya ƙara nuna haɗarin da ma’aikatan lafiya waɗanda ke sahun gaba ke fuskanta wajen kula da mutane da suka kamu da cutar.

Dangane da matakan da ake ɗauka, NCDC da abokan huldarta suna karfafa hanyoyin sa ido da rigakafin kamuwa da cutar da dakile kamuwa da ita tare da hada kai da ayyukan haɗin gwiwar al'umma a faɗin jihohin da abin ya shafa.

Hukumar ta ce ta horar da ma’aikatan kiwon lafiya da ke sahun gaba, tare da karfafa shirye-shiryen rigakafi da kuma hanyoyin dakile cutar da samar da kayayyakin kariya da aka tsara tare da tura Kungiyoyin Ba da Agajin Gaggawa na Kasa zuwa jihohi bakwai aka fi samun rahotannin cutar.

Haka kuma ta samar da wani Tsarin Kariya na Ma'aikatan Kiwon Lafiya na kwanaki 30 da nufin rage cututtuka masu yaduwa a tsakanin ma'aikatan da ke kan gaba a jihohin da aka fi fama da cutar, tare da tallafi daga Hukumar Lafiya ta Duniya da Cibiyar Kula da Cututtuka masu yaduwa ta Amurka.

Rumbun Labarai
’Yanbindiga sun kashe mutum 17 a Jihar Zamfara a Nijeriya
Sojojin Nijeriya sun kashe ’yanta’adda 25 a Borno, sun ƙwato makamai
Nijeriya ta rage dogaro da kuɗaɗen shiga daga ɓangaren man fetur sosai – Tinubu
Shugaba Tinubu da Christopher Musa sun sake nazari kan tsarin tsaro da kariya na Nijeriya
Nijeriya ta ayyana zaman makokin kwana uku kan sojojin da suka mutu a hatsarin jirgin sama a Ondo
Jirgin sama na sojin Nijeriya ya yi hatsari a Jihar Ondo
Malamai 300,000 daga 700,000 ne ba su da ƙwarewa a Nijeriya – Majalisar Rajistar Malamai
An kashe mutane 28 duk da dokar hana fita a jihar Filato a Nijeriya - Rahotanni
Gwamnonin Arewa maso-gabashin Nijeria sun yi shelar kafa kamfanin jiragen sama na yanki
Tinubu ya ceci Nijeriya daga wargajewa, in ji Kashim Shettima
Yawan iskar gas ɗin da Nijeriya ke samarwa a cikin gida ya ɗara ƙafa biliyan 2
Mutfwang ya gana da Tinubu, ya ce an fara gurfanar da masu kai hare-hare a Filato
'Yansandan Nijeriya sun ceto mutane 10 daga cikin 'yan NYSC da aka yi garkuwa da su a jihar Imo
Nijeriya: Mutane uku sun mutu a turmutsitsin rabon tallafin kuɗi a Jihar Neja
Ranar 'Yancin Kai a Nijeriya: Sauye-sauyen da muke yi za su haifar da sakamako mai kyau - Tinubu
Dubban fasinjojin Kano da suka bi Saudi Airline sun koka cewa kayansu sun maƙale a Saudiyya
Rundunar Sojin Nijeriya ta ƙaddamar da motocin yaƙi masu sulke da bataliyar soji uku a jihar Kebbi
'Yansandan Nijeriya sun gano ƙoƙon kawuna 28 a wani daji a Jihar Abia
Kotun Nijeriya ta umarci NMDPRA ta bai wa A.A Rano, AYM Shafa da Matrix lasisin shigo da fetur
An sace fiye da mutum 80 a cikin mako biyu a arewacin Nijeriya