| Hausa
DUNIYA
2 minti karatu
An kama mutane da dama bayan zanga-zangar ƙyamar Musulunci a Amurka
Mazauna birnin Dearbon na Jihar Michigan ta Amurka da masu goyon bayan Musulunci sun tunkari Jake Lang, mutumin da ya yi ƙaurin suna wurin zanga-zangar ƙin jinin Musulunci, lamarin da ya sa 'yansanda suka kama mutane da dama.
An kama mutane da dama bayan zanga-zangar ƙyamar Musulunci a Amurka
Masu zanga-zangar nuna adawa da Musulmai sun taru a birnin Dearborn na jihar Michigan, inda Musulmai suka fi rinjaye. / AFP

An kama mutane da dama bayan wata zanga-zangar nuna ƙyamar Musulmi da aka gudanar a birnin Dearborn da ke jihar Michigan ta Amurka, wanda mafi yawan mazaunansa Musulmai ne, inda zanga-zangar ta ja hankalin ɗaruruwan masu goyon bayan Musulunci.

Mai zanga-zangar nuna ƙyamar Musulunci, Jake Lang, da magoya bayansa sun taru a wajen ɗakin karatu na Henry Ford Centennial Library a ranar Talata domin wani taro da ya tallata a matsayin taron “Christian Crusader”, inda aka yi arangama tsakanin masu zanga-zangar ƙin jinin Musulunci da kuma masu goyon baya.

’Yansandan Dearborn sun tabbatar da kama mutane da dama, amma sun ce za a fitar da adadin ƙarshe daga baya.

Hukumomi sun tura ƙarin jami’an tsaro gabanin gudanar da zanga-zangar.

Magajin garin Dearbon, Abdullah Hammoud, ya bayyana irin tasirin zanga-zangar ga al’ummar Musulmin birnin, inda ya ba da labarin wata magana da ya yi da wani yaro mai kimanin shekara shida ko bakwai, inda yaron ya tambaye shi ko masu zanga-zangar sun zo ne domin su kashe shi.

“Yaranmu suna sauraronmu,” in ji Hammoud.

“Suna jin tattaunawarmu, suna ganin labaranmu, kuma suna lura idan iyayensu suna cikin damuwa.”

Bayan kwanaki ana samun ƙarin tashin hankali, Babbar Lauyar Jihar Michigan, Dana Nessel, ta tabbatar da cewa ma’aikatarta na aiki kai tsaye tare da Magajin Gari Hammoud, shugabannin birnin da kuma Sashen ’Yan Sandan Dearborn, inda take ba da cikakken goyon bayan gwamnatin jiha tare da gudanar da sa ido tare domin tabbatar da tsaron jama’a.

Lamarin ya kasance sabon misali a cikin jerin irin tsokanar da ake yi wa Musulmi da nuna ƙyama da Lang ya yi da gangan a Dearborn, da kuma tarzomar da ta faru a yayin jerin gwanon Arbaeen na shekara-shekara a farkon wannan watan.

Lang, wanda ya shiga cikin masu tayar da tarzoma na ranar 6 ga Janairu, wanda daga baya aka yi wa afuwa, ya sha gudanar da zanga-zangar nuna kyamar Musulunci a Dearborn.