Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya yi Allah-wadai da matakan da Isra’ila ta dauka kan ayarin jiragen ruwa na Global Sumud, yana bayyana su a matsayin “fashin teku da aikata ta’addanci,” tare da kira ga kasashen duniya su mayar da martani kan abin da ya kira “ayyukan Isra’ila na rashin bin doka.”
Da yake magana bayan taron Majalisar Ministoci a Ankara a ranar Litinin, Erdoğan ya ce tarewa da hare-haren da Isra’ila ta kai kan ayarin agaji ba za su raunana goyon bayan duniya ga Falasdinawa ba, ko ƙoƙarin neman adalci ga Gaza.
“Mun yi Allah-wadai da fashin teku da ta’addancin Isra’ila da tsananin kalamai mafi ƙarfi,” in ji Erdoğan, yana ƙara da cewa ayarin jirgin yana wakiltar aikin jinƙai da masu fafutuka daga ƙasashe kusan 40 suka goyi baya.
Shugaban Turkiyya ya kuma yi kira ga ƙasashen duniya su ɗauki matakai na zahiri kan ayyukan Isra’ila, tare da zargin Tel Aviv da ci gaba da keta dokar ƙasa da ƙasa ta hanyar killacewa da hare-hare kan Gaza.
An kai hari kan ayarin agaji
An shirya Global Sumud Flotilla ne a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ƙasashen duniya na kalubalantar killacewar da Isra’ila ta yi wa Gaza, tare da isar da agajin jinƙai ga Falasɗinawa da ke fuskantar ƙara taɓarɓarewar yanayin jinƙai bayan watanni na hare-haren Isra’ila a yankin.
Wannan aikin ya haɗa da masu fafutuka, likitoci da masu kare haƙƙin ɗan’adam da ke tafiya a cikin jiragen agaji dauke da kayayyakin jinƙai da aka tanada domin Gaza.
Turkiyya ta sha yin Allah-wadai da mummunan yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza, kuma tana daga cikin ƙasashen duniya da suka fi fitowa fili wajen kiran a tsagaita wuta nan take, a buɗe hanyoyin isar da agaji ba tare da cikas ba, da kuma a hukunta masu kai hare-hare kan fararen hula.
Ankara ta kuma goyi bayan ƙoƙarin shari’a na ƙasa da ƙasa da ake yi kan Isra’ila, tare da ƙara ƙaimi a diflomasiyyar da take yi domin ƙara matsin lamba kan Tel Aviv dangane da matsalar jinƙai a Gaza.















