Farfesa Isa Ali Pantami ya buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta wallafa sunansa a matsayin ɗan takarar jam’iyyar PDP na kujerar gwamnan Jihar Gombe a zaɓen 2027, bayan an cire sunansa daga jerin sunayen ‘yan takarar da hukumar ta fitar.
A cikin wata takardar ƙorafi da lauyoyinsa suka aika wa INEC ranar Litinin, 12 ga Oktoban 2026, Pantami ya ba hukumar wa’adin kwana biyu, zuwa ranar Laraba, 14 ga Oktoba, ta wallafa sunansa tare da sauran ‘yan takarar.
Lauyoyin, ƙarƙashin jagorancin Ahmed Raji, SAN, sun ce cire sunan Pantami daga jerin sunayen da INEC ta fitar ranar 10 ga Oktoba ya faru ne ba tare da bayyana dalili ba, duk da cewa a cewarsu, ya lashe zaɓen fitar da gwani na PDP da aka gudanar ranar 29 ga Satumba.
Takardar ta bayyana cewa Pantami ya lashe zaɓen fitar da gwani na farko da aka gudanar ranar 26 ga Mayun 2026, amma daga baya Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe ta soke zaɓen a hukuncin da ta yanke ranar 24 ga Satumba, tare da umartar PDP da ta sake gudanar da shi cikin kwanaki 30.
A cewar lauyoyinsa, jam’iyyar ta bi umarnin kotun ta hanyar gudanar da sabon zaɓen fitar da gwani ranar 29 ga Satumba, wanda Pantami ya sake lashewa. Sun kuma ce jami’an INEC sun halarci zaɓen domin sa ido, kuma an sake miƙa sunansa ga hukumar a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.
Lauyoyin sun kafa hujja da hukuncin kotun kan batun cancantar Pantami na zama ɗan jam’iyyar PDP, suna mai cewa umarnin kotun na soke zaɓen farko ya shafi zaɓen na ranar 26 ga Mayu ne, ba sabon zaɓen da aka gudanar a watan Satumba ba.
Sun kuma yi zargin cewa INEC ba ta da ikon cire sunan ɗan takarar da jam’iyya ta tsayar sai bisa tsarin doka, inda suka buƙaci hukumar ta ɗauki matakin gyara tare da sanar da su a rubuce kan matakan da ta ɗauka.
Sai dai har zuwa lokacin da aka fitar da wannan rahoto, ba a samu martanin INEC kan ƙorafin ba.
Pantami, tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani na Nijeriya, na neman tikitin PDP domin takarar gwamnan Jihar Gombe a zaɓen 2027.























