| Hausa
KIMIYYA DA FASAHA
3 minti karatu
Amurka ta sauya wa kayayyakin sojinta wuri, ta rage shiga sansaninta mafi girma a Gabas ta Tsakiya
Washington tana ƙarfafa kariya ga dakarunta ta hanyar sauya wa kayakkain yaƙinta wuri, yayin da Iran ta yi gargaɗin martani mai ƙarfi idan Amurka ta shiga hare-haren Isra’ila kai-tsaye.
Amurka ta sauya wa kayayyakin sojinta wuri, ta rage shiga sansaninta mafi girma a Gabas ta Tsakiya
Rundunar sojin Amurka ta sauya wa jiragen sama da na ruwa wuri domin kare dakarunta a Gabas Ta Tsakiya / Reuters

Rundunar sojan Amurka ta ɗauke wasu jiragenta na sama da na ruwa daga wasu sansanoni da Iran za ta iya kai wa hari cikin sauƙi a Gabas ta Tsakiya, kamar yadda jami’an Amurka biyu suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters ranar Laraba.

Matakan na zuwa ne yayin da Shugaba Donald Trump ya sa duniya take jiran ko Amurka za ta fara taimakawa wajen kai hare-hare kan tashoshin nukiliyar Iran da kuma tashoshin makamai masu linzaminta yayin da mutane suka tserewa daga baban birnin ƙasar a rana ta shida da fara hare-hare ta sama.

A wani ɓangaren kuma, ofishin jakadancin Amurka a Qatar ya bada sanarwa ranar Alhamis cewa zai taƙaita iya yadda jami’anta za su iya shiga sansanin sojin sama na Al Udeid, sansanin sojin Amurka mafi girma a Gabas ta Tsakiya, wanda ke cikin hamada a waje birnin Doha.

Ofishin jakadancin ya shaida wa jami’ai da kuma ‘yan ƙasar Amurka su mayar da hankali sosai “wajen yin taka-tsantsan game da rikicin da ke faruwa a yankin ".

Jami’an biyu, waɗanda suka yi magana bisa sharaɗin sakaya sunayensu, sun ce sauya wa jiragen sama da na ruwa wuri wani ɓangare ne na kare dakarun Amurka, amma sun ƙi su bayyana jirage nawa aka sauya wa wurare ko kuma inda aka kai su.

Ɗaya daga cikin jami’an ya ce an ɗauke jiragen da ba sa cikin wuri mai ƙarfi daga sansanin sojin Al Udeid kuma an ɗauke jiragen sojin ruwa daga tashar jiragen Ruwa ta Bahrain inda ayarin jiragen ruwan sojin na biyar yake.

"Ba wani abin da ba a saba gani ba ne," in ji jami’in. "Kare dakaru shi ne abin da aka fi bai wa muhimmanci."

An kai kayayyakin yaƙin ruwan Amurka zuwa Gabas Ta Tsakiya

Reuters ta ba da rahoto a wannan makon game da tafiyar jirgin da ke kara wa jiragen sama mai zuwa Turai da kuma sauran kayayyakin yaƙi zuwa Gabas Ta Tsakiya, ciki har da ƙarin jiragen yaƙi.

Wani jirgin ruwa mai dakon jiragen sama na yaƙi na kan hanyarsa zuwa Gabas Ta Tsakiya.

Isra’ila ta ƙaddamar da yaƙi ta sama ranar Juma’a bayan ta ce ta yi imanin cewa Iran ta kusa samar da makamin nukiliya.

Iran ta musanta kera makaman nukiliya.

Iran ta sanar da Washington cewa za ta mayar da martani da ƙarfi ga Amurka idan ta shiga yaƙin Ira’ila kai-tsaye, kamar yadda Jakadan Iran a Majalisa Ɗinkin Duniya ya bayyana a birnin Geneva ranar Laraba.

 

 

Rumbun Labarai
Gidauniyar Gate da OpenAI sun ƙaddamar da shirin inganta lafiya ta hanyar fasahar AI a Afirka
Ɗan sama jannatin da ya kamu da rashin lafiya ya sa dole jirgin NASA ya dawo duniya
Duniyar dijital: Yadda annobar son waya da komfuta ke hana yara jin daɗin ƙuruciya da samun kulawa
Jirgin sama jannati mai zagaye sararin samaniya na farko da aka ƙera a Turkiyya zai fara aiki
Butum-butumin NASA ya ɗauki yadda aka yi walƙiya a duniyar Mars a lamarin da ba a taɓa gani ba
Masanin kimiyya na Turkiyya ya jagoranci 'yan sama jannati wajen gano sabbin duniyoyi
An fara baje-kolin fasahar jiragen sama ta TEKNOFEST a Istanbul
Hatsarin da ke tattare da gem din Roblox ga yara ya sa Saudiyya da UAE haramta shi
Hirar Xi da Putin kan tsawon rayuwa har shekara 150: Shin ilimin kimiyya ya kai wannan matakin?
An kai Agushi sararin samaniya ya yi kwana bakwai don yin binciken kimiyya a kansa
Afirka za ta iya zama 'kan gaba a fannin sabunta makamashi': Sakatare Janar na MDD
Iyakar ikon kasashe kan Kirkirarriyar Basira da abin da hakan ke nufi ga tsarin tafiyar da duniya
Grok ta dawo aiki bayan dakatar da ita don bankaɗar da ta yi kan kisan ƙare dangi na Gaza
Kirkirarriyar Basira na ƙoƙarin magana da harsunan Afirka, Ko ƙarshen watsi da harsunan ya zo?
WhatsApp ya rufe shafuka fiye da miliyan 6.8 masu alaƙa da zamba: Meta
Google ya amince tsarin gargaɗinsa ya gaza ceton miliyoyin mutane a girgizar ƙasar Turkiyya a 2023
Masana kimiyya sun ɗauki hoton da ba a saba gani ba na mutuwar taurari a kaunu
Meta na tattaunawa da kamfanin Scale AI domin zuba jarin fiye da dala biliyan 10 — rahoto
Masu fafutuka suna son a sauya tsarin TikTok saboda gazawar shafin daga kare yara
Ɓoyayyun duwatsun astiriyod na duniyar Venus za su iya faɗowa duniyarmu - Bincike