| Hausa
DUNIYA
3 minti karatu
Saudiyya da Isra'ila za su Amurka don tattaunawa yayin da Trump ke tura jiragen yaƙi na ruwa Iran
Shugaban hukumar leƙen asirin Isra'ila zai yi wa Washington karin bayani kan yiwuwar kai hari Iran, yayin da jami'an Saudiyya ke neman mafita ta diflomasiyya don kauce wa yaki a yankin, kamar yadda kafar Axios ta rawaito.
Saudiyya da Isra'ila za su Amurka don tattaunawa yayin da Trump ke tura jiragen yaƙi na ruwa Iran
Amurka da ƙawarta Isra'ila su ma sun fusata da shirin makami mai linzami na Iran. / AP
30 Janairu 2026

Jami'an tsaro da na hukumar leken asiri daga Isra'ila da Saudiyya za su ziyarci Amurka a wannan makon don tattaunawa kan Iran a daidai lokacin da sojojin Amurka ke ci gaba da isa yankin, kamar yadda shafin labarai na Axios ya ruwaito.

Janar Shlomi Binder, shugaban leken asirin sojojin Isra'ila, ya gudanar da wasu jerin zaman shawarwari na manyan jami'ai a ranar Talata da Laraba tare da manyan shugabannin Pentagon, CIA da Fadar White House, in ji Axios, yana mai ambato wasu jami'an Amurka biyu.

Ana sa ran tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan ba da takamaiman bayanan sirri da gwamnatin Trump ta nema, gami da bayanai kan yiwuwar kai hari a Iran.

A ɓangare guda kuma, ana sa ran Ministan Tsaron Saudiyya Yarima Khalid bin Salman zai jaddada hanyoyin diflomasiyya a yayin ganawarsa ta ranar Alhamis da Juma'a da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio da wakilin Amurka Steve Witkoff da kuma jami'an Pentagon.

Ma'aikatar Tsaron Saudiyya ta ce Yarima Khalid da tawagar da ta yi masa rakiya sun isa Washington a ziyara da ta mayar da hankali kan "tattaunawa kan dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu masu ƙawance da kuma hanyoyin da za su ƙarfafa juna ,tare da taɓo batutuwan da suka shafi ƙasashen biyu."

Ƙaruwar ayyukan diflomasiyya

Saudiyya, wacce ke a tsakiya wajen isar da saƙonni tsakanin Washington da Tehran, ta ce a baya ba ta yarda Amurka ta yi amfani da sararin samaniyarta wajen kai hari a Iran ba.

Hakan na zuwa ne yayin da Amurka ta aika tawagar jiragen sama ta USS Abraham Lincoln don kammala isowar manyan jiragen "rundunar sojin ruwa na ƙasar" da Shugaba Donald Trump ya yi iƙirarin sun "fi girma" idan aka kwantata da rundunar da aka tura Venezuela kwanan nan.

"Umarnin a yanzu shi ne a shirya," in ji wani jami'in Amurka, yana mai nuna cewa shugaban Trump na gab da yanke shawara ta ƙarshe kan matakin soji da za a dauka.

Trump ya buƙaci Iran ta cim ma yarjejeniya kan shirin nukiliyarta kafin lokaci ya kure, yana mai gargaɗin cewa a wannan karon hari zai "fi muni."

Amurka ta kai hari kan wuraren nukiliyar Iran har guda uku a watan Yuni a lokacin yaƙin kwanaki 12 da Tehran ke yi da Isra'ila,

Iran ta ce shirin nukiliyarta na farar hula na dalilan zaman lafiya ne, amma ƙasashen yamma sun kafa sun tsare kan cewa tana ƙera makamin nukiliya ne.

Shirin makami mai linzami na Iran dai ya fusata Amurka da ƙawarta Isra'ila.

Rumbun Labarai
Chadi za ta tura sojoji 750 domin yaƙar 'yandaban Haiti
Trump: Amurka na duba yiwuwar 'kammala' hare-haren soji kan Iran
NATO na fuskantar ‘mummunar makoma’ idan ƙasashenta suka ƙi taimaka wa Amurka a yaƙin Iran - Trump
Trump ya ce bai shirya yin yarjejeniya ba domin kawo ƙarshen yaƙin Iran
Tsarin kiwon lafiya a Gabas ta Tsakiya na fuskantar barazana yayin da rikici ke ƙara muni: WHO
Kusan rabin rahotannin kafafen watsa labaran Birtaniya kan Musulmi na dauke da nuna wariya
Mashigar Hormuz: Hanyar ruwan da za ta iya girgiza tattalin arzikin duniya
Dalilai huɗu da suka sa matasan Afirka suka fi lafiyar ƙwaƙwalwa a duniya
Musulmai a Turkiyya, Oman, Singapore, da Australia za su fara azumin Ramadan a ranar Alhamis
'Babu wani takamaiman abin da aka cim ma' a ganawar Trump da Netanyahu a kan Iran
An ci tarar ƙananan hukumomi 10 a Holland kan binciken al'ummomin Musulmai ba tare da saninsu ba
Trevor Noah: Trump ya yi barazanar maka mai gabatarwa a Gasar Grammy a Kotu
WHO: Amurka ta fita daga Hukumar Lafiya ta Duniya bayan shekara 78
Masana kimiyya sun gano zanen shacin hannu 'mai shekara 67,800' a wani kogo a Indonesia
Ministan Wajen Saudiyya da takwarorinsa na Iran, Oman da Qatar sun tattauna kan zaman lafiyar yanki
Amurka ta dakatar da ba da bizar masu ƙaura ga 'yan Nijeriya da wasu ƙasashe 74
Wani sanatan Amurka ya yi gargaɗi kan ƙaruwar ƙyamar Musulunci da ƙin jinin Larabawa
Trump ya saka harajin kashi 25 kan ƙasashen da ke kasuwanci da Iran
An katse intanet da wayoyin hannu a Iran
Matar shugaban Turkiyya ta gana da shugaban UNRWA kan shirin buɗe ofis a Ankara