| Hausa
SIYASA
2 minti karatu
Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara a Nijeriya ya fice daga PDP zuwa APC
Gwamnan Jihar Zamfara a Nijeriya, Dauda Lawal ya sanar da ficewarsa daga Jam’iyyar zuwa jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar, sakamakon rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar.
Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara a Nijeriya ya fice daga PDP zuwa APC
Dauda Lawal / Others
9 Maris 2026

Gwamnan Jihar Zamfara a Nijeriya, Dauda Lawal ya sanar da ficewarsa daga Jam’iyyar zuwa jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar, sakamakon rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar.

An sanar da wannan mataki ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ranar Litinin a dakin taro na Rescue Hall da ke Gidan Gwamnatin jihar a Gusau. Mataimakin gwamnan jihar, Mani Mummuni, ne ya jagoranci taron, inda shugabannin siyasa da sauran masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na jihar suka halarta.

Da yake magana a madadin gwamnan, mataimakin gwamnan ya ce an dauki wannan mataki ne bayan shawarwari masu zurfi da kuma duba halin da jam’iyyar PDP ke ciki.

“Bayan sauraron shawarwarinku da yin nazari mai zurfi, musamman bukatar samun hadin kai a tsakanin manyan ‘yan siyasa domin magance matsalolin tsaro a jihar, Mai Girma Gwamna Dauda Lawal ya yanke shawarar komawa jam’iyyar APC,” in ji shi.

Ya kuma umarci dukkan masu rike da mukaman siyasa da ke goyon bayan gwamnan da su gaggauta ajiye mukamansu na PDP, su kuma shirya yin rajista da APC da zarar an sake bude rajistar ta intanet.

A cewarsa, shugabancin siyasar jihar na da burin kara rajistar sabbin mambobin APC har 400,000 a cikin kwanaki 17 masu zuwa a jihar.

Wannan mataki ya biyo bayan wasu shawarwari da tuntuɓa na jiha baki daya da Gwamna Lawal ya kaddamar a watan Janairu domin tantance makomar siyasar jihar, a daidai lokacin da rikicin PDP ke kara tsananta, tare da la’akari da shirye-shiryen babban zaben 2027.

Gwamna Lawal ya kuma gode wa jam’iyyar PDP bisa damar da ta ba shi na tsayawa takarar gwamna a zaben 2023, inda ya ce ya yi kokari wajen sasanta rikicin cikin gida na jam’iyyar, amma hakan bai yi nasara ba.

Ya kuma gode wa al’ummar Zamfara bisa goyon baya da kaunar da suke nuna masa, tare da tabbatar musu cewa manufar gwamnatinsa ta “Rescue Agenda” za ta ci gaba da tafiya yadda aka tsara duk da sauyin jam’iyyar.

 

Rumbun Labarai
Trump ya bar ƙofar Iran a bude, kuma Netanyahu ba zai iya rufe ta ba
Yadda 'yan Nijeriya suka fusata kan matakin Amurka na saka wa Kwankwaso takunkumi
Majalisar Dattijan Nijeriya ta amince da tsarin aika sakamakon zabe kai-tsaye ta intanet
Taƙaddama a kan gyaran dokar zaɓe ta Nijeriya
Ghana ta yi wa jakadanta a Nijeriya kiranye kan zargin maguɗin zaɓe
Iran ta ce ta shiga tattaunawar Oman da Amurka da 'kyakkyawar niyya'
Masar da Saudiyya sun yi kira ga samar da hanyoyin da suka dace kafin tattaunawar Amurka da Iran
Greenland ba hajar sayarwa ba ce
Yayin da duniya ta koma kasuwar buƙatar diflomasiyya, wai zai tsaya wa ƙasashe marasa ƙarfi a 2026?
Amurka ta dakatar da bai wa ‘yan Nijeriya biza
Alkawarin dala miliyan 150 zai sake gina Aleppo da yaƙi ya lalata
Yadda 'nadamar zalunci' ke janyo rushewar lafiyar ƙwaƙwalwa a rundunar sojin Isra’ila
Me ya sa Trump da masu sharhi da ke da ra’ayin rikau ke sa ido kan al’ummar Somalia da ke Minnesota?
Shugaban Nijar Tiani ya karɓi shugaban Bilma bayan ya yi watanni 16 a hannun masu garkuwa da mutane
An daƙile harin RSF kan West Kordofan: Rundunar Sojin Sudan
Nijar ta ce ta fara kai uranium ɗinta kasuwar duniya
Trump ya ce Amurka za ta dakatar da hijirar 'yan cirani daga kasashe marasa arziki har abada
Gobarar Hong Kong: Adadin waɗanda suka mutu ya kai 128 yayin da aka shiga kwana uku a ƙoƙarin ceto
China ta yi gargaɗin 'murƙushe' katsalandan ɗin ƙetare kan shirin makami mai linzani na Japan
Yaƙin Sudan: Maye gurbin UAE da Turkiyya na iya ƙarfafa ƙoƙarin ƙasashe na samar da zaman lafiya