| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
1 minti karatu
Rundunar sojin Yemen ta ce ta kashe 'yan Houthi 260 a hare-haren Taiz da Lahj
Rundunar sojin ta kuma bayyana cewa an lalata gomman motocin 'yan Houthi yayin da ake zafafa musayar wuta cikin yaƙin da ake yi a Yemen.
Rundunar sojin Yemen ta ce ta kashe 'yan Houthi 260 a hare-haren Taiz da Lahj
Sojojin gwamnatin Yemen suna tafiya cikin akori kura kusa da fagen yaƙin Jabal Han, a yammacin birnin Taiz, ranar 3 ga watan Oktoba na shekarar 2026.

Rundunar sojin Yemen ta bayyana ranar Lahadi cewa an kashe ‘yan Houthi 260 a jerin samame 97 kan masu kai ɗaukin soji a fagagen yaƙi a lardunan Taiz da Lahj.

Mai magana da yawun sojin Kanal Majed al Nuzaili ya ce jerin samen sun yi aiki ne da jiragen yaƙi da jirage mara matuƙa da manyan bindigogi da makamai masu linzami da maharba.

Ya ƙara da cewa an lalata motocin soji da motocin sufuri da kayayyakin dako da 44 ne aka lalata.

Sanarwar na zuwa ne sa’o’i bayan rundunar sojin ta ce aƙalla ‘yan Houthi 700 ne aka kashe a samame 257 a fagagen yaƙi.

Kuma ba a sami tsokaci ba daga ‘yan Houthi game da sanarwar sojin.

Yemen ta kasance cikin rikici tun lokacin da ‘yan Houthi suka karɓe iko da babban birnin ƙasar Sanaa, da sauran lardunan a shekarar 2014, lamarin da ya sa ƙawancen da Saudiyya ke jagoranta ta shiga lamarin a shekarar 2015 domin goyon bayan gwamnatin da ƙasashen duniya suka yarda da ita.

Wata yarjejeniyar tsagaita wuta ta shekarar 2022 ta rushe a watan Yuli, kuma yaƙi ya ƙaru sosai tun wancan lokacin.