| Hausa
DUNIYA
2 minti karatu
An katse intanet da wayoyin hannu a Iran
Kungiyar sanya idanu ta NetBlocks ta ce alkaluma sun nuna Iran na fuskantar katsewar internet a fadin kasar.
An katse intanet da wayoyin hannu a Iran
Wata kungiyar kare hakkin dan adam da ke sa ido kan Iran ta ba da rahoton cewa masu zanga-zanga da dama sun mutu. / Reuters
9 Janairu 2026

Iran na fuskantar katsewar intanet a faɗin ƙasar, inda rahotanni ke nuna cewa an katse ayyukan sadarwa da amfani da wayar hannu.

"Bayanai na kai-tsaye sun nuna cewa a yanzu Iran tana cikin tsakiyar katsewar intanet a dukka faɗin ƙasar," in ji ƙungiyar sa ido kan intanet ta NetBlocks da ke Landan a wata sanara ta shafin X a ranar Alhamis.

Rahotannin kafofin watsa labarai sun ce an katse ayyukan wayar hannu jim kaɗan bayan rufe intanet, ko da yake hukumomin Iran ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba.

An ruwaito cewa katsewar ta biyo bayan gudanar da zanga-zanga a Iran tun daga ƙarshen Disamba, wanda ke da alaƙa da faɗuwar darajar kuɗin ƙasar da kuma ƙalubalen tattalin arziki da ke ci gaba da fuskantar ƙasar.

Adadin waɗanda suka mutu sakamakon zanga-zangar da ake yi a Iran ya ƙaru zuwa 38, kamar yadda wata ƙungiyar kare hakkin ɗan’adam da ta mayar da hankali kan Iran ta ruwaito a ranar Laraba.

Zanga-Zanga ta bazu a fadin kasar

Iran ta fuskanci zanga-zanga mai yawa tun daga watan da ya gabata, wadda aka fara daga ranar 28 ga Disamba a babbar kasuwar Tehran, saboda raguwar darajar kuɗin Iran da kuma taɓarɓarewar tattalin arziki.

Daga baya zanga-zangar ta bazu zuwa wasu birane da dama a faɗin ƙasar.

Wata ƙungiyar kare hakkin ɗan’adam da ke sa ido kan Iran ta ba da rahoton cewa masu zanga-zanga da dama sun mutu.

Hukumomin Iran ba su tabbatar da adadin waɗanda suka mutu ba ko kuma sun bayar da cikakkun bayanai game da waɗanda suka mutu ko suka jikkata.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran a ranar Laraba ta yi Allah wadai da "shisshigi a harkokin cikin gidan Iran" da Amurka ta yi a tsaka da zanga-zangar da ake yi a birane daban-daban.

Tehran ta jaddada a cikin wata sanarwa a shafin intanet na Ma'aikatar Harkokin Wajen cewa Amurka "tana da ƙiyayya ga al'ummar Iran" kuma ta yi Allah wadai da abin da ta bayyana a matsayin ɗabi'u da manufofin Amurka game da Iran.

 

Rumbun Labarai
Chadi za ta tura sojoji 750 domin yaƙar 'yandaban Haiti
Trump: Amurka na duba yiwuwar 'kammala' hare-haren soji kan Iran
NATO na fuskantar ‘mummunar makoma’ idan ƙasashenta suka ƙi taimaka wa Amurka a yaƙin Iran - Trump
Trump ya ce bai shirya yin yarjejeniya ba domin kawo ƙarshen yaƙin Iran
Tsarin kiwon lafiya a Gabas ta Tsakiya na fuskantar barazana yayin da rikici ke ƙara muni: WHO
Kusan rabin rahotannin kafafen watsa labaran Birtaniya kan Musulmi na dauke da nuna wariya
Mashigar Hormuz: Hanyar ruwan da za ta iya girgiza tattalin arzikin duniya
Dalilai huɗu da suka sa matasan Afirka suka fi lafiyar ƙwaƙwalwa a duniya
Musulmai a Turkiyya, Oman, Singapore, da Australia za su fara azumin Ramadan a ranar Alhamis
'Babu wani takamaiman abin da aka cim ma' a ganawar Trump da Netanyahu a kan Iran
An ci tarar ƙananan hukumomi 10 a Holland kan binciken al'ummomin Musulmai ba tare da saninsu ba
Trevor Noah: Trump ya yi barazanar maka mai gabatarwa a Gasar Grammy a Kotu
Saudiyya da Isra'ila za su Amurka don tattaunawa yayin da Trump ke tura jiragen yaƙi na ruwa Iran
WHO: Amurka ta fita daga Hukumar Lafiya ta Duniya bayan shekara 78
Masana kimiyya sun gano zanen shacin hannu 'mai shekara 67,800' a wani kogo a Indonesia
Ministan Wajen Saudiyya da takwarorinsa na Iran, Oman da Qatar sun tattauna kan zaman lafiyar yanki
Amurka ta dakatar da ba da bizar masu ƙaura ga 'yan Nijeriya da wasu ƙasashe 74
Wani sanatan Amurka ya yi gargaɗi kan ƙaruwar ƙyamar Musulunci da ƙin jinin Larabawa
Trump ya saka harajin kashi 25 kan ƙasashen da ke kasuwanci da Iran
Matar shugaban Turkiyya ta gana da shugaban UNRWA kan shirin buɗe ofis a Ankara