Dakarun Operation HADIN KAI sun ceto fararen-hula 53 tare da kwato motoci takwas bayan sun tarwatsa wani shingen hanya da ake zargin mayakan Boko Haram/Daesh-WAP ne suka kafa a kan hanyar Buratai zuwa Kamuya da ke Ƙaramar Hukumar Biu a Jihar Borno.
A cewar rundunar sojin, an gudanar da wannan samame ne a ranar Laraba, 24 ga Yuni, inda dakarun runduna ta musamman ta Bataliya ta 135 ne suka gudanar da wannan aikin a ci gaba da hare-haren da ake kai wa 'yan ta'adda a yankin Arewa maso Gabas.
Rundunar ta ce dakarun da ke jibge a Dutse Kura sun hango waɗanda ake zargin suna tare hanyar ne ta hanyar na'urorin sa ido. Daga nan ne aka tura tawagar gaggawa ta Quick Reaction Force (QRF), wadda ta bi sawun 'yanta'addan zuwa yankin Mangari–Dora.
Sojojin sun ce sun yi artabu da 'yanta'addan, lamarin da ya tilasta musu janyewa cikin rudani.
Bayan kammala aikin, dakarun sun ceto fararen-hula 53 tare da ƙwato motoci takwas da aka ce 'yanta'addan sun ƙwace. Har ila yau, sun bi hanyar da maharan suka gudu domin tabbatar da tsaro tare da gudanar da bincike a yankin, sai dai ba su sake cin karo da su ba.
An kai dukkan mutanen da aka ceto, tare da motocin da sauran kadarorin da aka ƙwato daga hannun ‘yanta’addan cikin aminci zuwa garin Buratai. Rundunar ta ce ana ci gaba da tantance waɗanda aka ceto tare da yi musu gwaje-gwajen lafiya.
Hedikwatar Operation HADIN KAI ta yaba wa dakarun bisa abin da ta bayyana a matsayin ƙwarewa da kuma gaggawar ɗaukar mataki wajen gudanar da aikin.
Rundunar ta kuma buƙaci al'ummar da ke yankin da take ayyukan da su ci gaba da kasancewa cikin shiri tare da bai wa jami'an tsaro bayanai cikin gaggawa kan duk wani motsi ko aiki da suke zargi.
A cewar rundunar, halin tsaro a yankin ya kasance cikin kwanciyar hankali, yayin da dakarun ke ci gaba da gudanar da sintiri da kuma mamaye yankunan domin hana sake aukuwar hare-haren 'yanta'adda.










