Tsawon shekaru da dama, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya gina sunansa na siyasa a matsayin mai tsaron gida - wata siffa mai ƙarfi da ta taimaka masa ya lashe zaɓe a jere kuma ta sanya shi zama firayminista mafi daɗewa a ƙasarsa.
Netanyahu zai sake tsayawa takara a zaɓe yayin da Isra'ila za ta fita rumfunan zaɓe a watan Oktoba.
Amma wani sabon bincike ya nuna cewa sake zaɓensa a yanzu na cikin shakku.
Wani bincike da aka gudanar a Channel 12 ta ƙasar ta Cibiyar Midgam, ɗaya daga cikin manyan kamfanonin bincike na kasuwa da ra'ayoyin jama'a a Isra'ila, ya nuna cewa kashi 43 cikin ɗari na 'yan Isra'ila za su fi son ganin Gadi Eisenkot, tsohon shugaban rundunar sojojin Isra'ila, a matsayin firaminista.
A akasin haka, kashi 34 cikin ɗari na Isra'ilawa ne kawai ke goyon bayan Netanyahu a matsayin firaminista.
A cewar binciken, Yashar, ana hasashen sabuwar jam'iyyar siyasa ta Eisenkot za ta lashe mafi yawan kujeru (23), Jam'iyyar Likud ta Netanyahu za ta yi nasara da kujeru 22, idan aka gudanar da zaɓe yanzu.
Ana sa ran cewa babban kawancen da ke adawa da Netanyahu zai lashe kujeru 59 a majalisar Knesset, wanda ya yi ƙasa da rinjayen (kujeru 61). A akasin haka, binciken ya nuna cewa jimillar kujeru 51 na jam'iyyun da ke goyon bayan Netanyahu ne.
Da farko, adadin ba zai yi kama da abin mamaki ba. Amma sun bayyana raguwar darajar tsaron Netanyahu a siyasar Isra'ila.
Masu sharhi sun danganta raunin da Netanyahu ya samu a fannin tsaro da fiye da shekaru biyu da rabi na yaƙin kare dangi a Gaza, baya ga yaƙe-yaƙen da aka yi a baya-bayan nan da Lebanon da Iran.
Arik Rudnitzky na Cibiyar Moshe Dayan ta Jami'ar Tel Aviv ya ce Netanyahu ya shafe shekaru yana ɗaukar kansa a matsayin "Malam Tsaro".
"A wajen Isra'ilawa da yawa, wannan hoton ya sha wahala sosai bayan abubuwan da suka faru a ranar 7 ga Oktoban 2023, musamman saboda Netanyahu bai taɓa ɗaukar alhakin gazawar da ya haifar da harin ba," Rudnitzky ya shaidawa TRT World.
Ta shaida wa TRT World cewa tsarin da ya daɗe yana bi na tafiyar da rikicin Falasdinu maimakon warware shi da kuma dogaro kan fasahar tauna tsakuwa aya ta ji tsoro" ya ruguje cikin kwana ɗaya".
Sakamakon ya kasance wani abu mai sauri kuma mai ɗorewa da ya doki kimar Netanyahu kan batun wanda ya fayyace aikinsa tsawon shekaru da dama.
Tun daga lokacin Firaministan Isra'ila ya yi ƙoƙarin sake gina kimarsa da ya rasa a ranar 7 ga Oktoba, 2023, ta hanyar yaƙe-yaƙe da yawa, waɗanda ba sa ƙarewa.
Tel Aviv ta kai hari kan ƙasashe shida, ciki har da Falasdinu, Iran, Lebanon, Qatar, Siriya, da Yemen, tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023.
Ceylan ta bayyana dabarun Netanyahu a matsayin yunƙurin sake tsara labarin: daga shugaban "wanda ya bar ranar 7 ga Oktoba ta faru" zuwa "shugaba ɗaya tilo da ya isa ya tinkari wa Iran".
Rudnitzky ya yarda cewa wasu ‘yan kasar Isra'ila na yaba wa Netanyahu kan ƙaddamar da yaƙi kan Iran.
Duk da haka, Netanyahu yana ci gaba da fuskantar suka mai zafi game da yadda Isra'ila ke tafiyar da iyakarta ta arewa, inda Hizbullah ta sami nasarar sake gina wasu daga cikin ƙarfinta kuma tana ci gaba da haifar da babban ƙalubalen tsaro, in ji shi.
Masu sharhi sun ce ‘yan kasar Isra’ila gama-gari ba za su yi watsi da wadannann kuɗaɗen da ake kashewa a waɗannan yaƙe-yaƙen da suka yi karo da juna ba. Harba makaman roka da makami mai linzami na dogon lokaci ya gwada fagen daga ta hanyoyin da ba a iya gani cikin shekaru da dama.
Rudnitzky ya nuna sakamakon da aka samu a hukumance, gami da rahoton babban jami’in kasar ta Janairu 2026, wanda ya nuna cewa al'ummomi da yawa - har yanzu ba su da isasshen matsuguni da kayayyakin more rayuwa na gaggawa.
Kimanin kashi ɗaya bisa uku na mazauna Isra'ila "ba su da cikakkiyar kariya daga hare-haren makamai masu linzami", a cewar rahoton babban jami’in kasar.
Rudnitzky ya ce tsaro ba wai kawai yana nufin shirya sojoji don yaƙi ba ne.
Ya ƙara da cewa "Hakan na nufin tabbatar da cewa fararen hula na da karfin halin juriya na tsawon lokaci na rashin tabbas, rudani, da rashin tsaro."
Shin an gaji da yakin ne?
Ceylan ta nuna irin tasirin tattalin arziki da na kashin kai da yaƙe-yaƙen da Netanyahu ya yi ke da shi a kan jama'ar Isra'ila: yawan kashe kuɗi da ake yi a fannin tsaro, yawan kiran 'yan kasa da aka ware su tafi yaki da hauhawar farashin kayayyaki wanda duk sun "ruguza tunanin rayuwa ta yau da kullum" ta ‘yan ƙasar.
Ta ce mafi illa daga cikin lamarin shi ne rikicin tsare fursunonin yaki.
A wajen adadi mai yawa na ‘yan kasar Isra'ila, kin amincewa da Netanyahu na fifita dawowar waɗanda aka yi garkuwa da su "ana ɗaukarsa a matsayin cin amana".
"Ana ganin Netanyahu da kansa ne ke da alhakin mutuwar waɗanda aka yi garkuwa da su," in ji ta.
Dogaronsa ga abokan hulɗarsa na dama kamar Itamar Ben-Gvir, ministan tsaron ƙasa na Isra'ila, ya ƙara rage masa kira, yana kulle shi cikin wani mawuyacin hali na siyasa, in ji ta.
Yaƙe-yaƙen da ba sa ƙarewa a Isra'ila a fannoni da dama ba su kawar da tsaro daga manufar ƙasa ba. Madadin haka, sun faɗaɗa abin da Isra'ilawa ke nufi da kalmar, in ji masu sharhi.
Rudnitzky ya ce masu jefa ƙuri'a yanzu ba wai kawai suna buƙatar ƙarfin soja ba, har ma da ɗaukar nauyi, jagoranci mai ƙwarewa, bayyana gaskiya, da kuma son daukar darasi daga gazawar da suka gabata.
Amincewar jama'a ga sojoji ita kanta ta yi tsauri sosai, galibi saboda kwamandojin soja sun karɓi alhakin kuma sun wallafa bincike kan gazawar ranar 7 ga Oktoba, in ji shi.
Duk da haka, ana ganin shugabannin siyasa a Isra'ila a matsayin waɗanda ba su da alaƙa da waɗannan saka rai, in ji shi.
Ceylan ta ce ƙoƙarin da Netanyahu yake yi na mayar da zargi ga sojojin Isra'ila da hukumomin leƙen asiri yayin da yake kare majalisar ministocinsa ya mayar da sojoji "jakar siyasa don tsirar Bibi".
A cikin wannan tsari, ya raba ‘yan Isra'ila masu ra'ayin addini da masu matsakaicin ra'ayi.
Yanayin jama'a ya koma ga ɗaukar alhaki ba tare da barin tsaro a matsayin babban abin damuwa ba, in ji ta.
Ma'anar tsaro da kanta ta canza. Abin da masu jefa ƙuri'a yanzu suka bayyana suna so shi ne "shugabancin tsaro mafi ƙwarewa, mai aiki, kuma mai riƙon amana" - halaye da Isra'ilawa da yawa ke dangantawa ga Eisenkot.
"Za mu iya cewa zaɓen Oktoba ba zai zama muhawara tsakanin yaƙi da zaman lafiya ba," in ji ta.
Ta ƙara da cewa, "Zai zama kuri'ar raba gardama kan ƙwarewa, mutuncin mutum, amincewa da cibiyoyi idan aka kwatanta da tseratar da akida."














