UNESCO ta gabatar da ƙudurin  saka ƙona Alƙur'ani a matsayin laifi / Photo: AP Archive

Dangane da shawarar da Ankara ta gabatar, babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya sanya wulaƙanta litattafai masu tsarki da suka haɗa da Alƙur'ani a wani daftarin ƙudurin da ya shafi wariyar launin fata da laifukan ƙiyayya, in ji Turkiyya.

Wakiliyar dindindin ta Ankara a UNESCO, Gulnur Aybet ta fada a ranar Juma'a cewa "a karkashin jagorancin Turkiyya, mun ƙara da ƙudurin Majalisar Dinkin Duniya da ke ayyana laifukan cin zarafin litattafai masu tsarki a matsayin keta dokokin kasa da kasa a cikin daftarin shawarar UNESCO.

“Yayin da nake bayyana goyon bayanmu na yaƙar duk wani nau’in laifuka na nuna ƙyama, na jaddada karuwar laifukan da ke da alaƙa da ƙiyayya ga Musulunci a ‘yan shekarun nan.

"Na lura cewa ya kamata UNESCO ta yi aiki daidai da ƙudurorin Majalisar Dinkin Duniya game da wannan. An amince da daftarin ƙudurin tare da gyare-gyaren da muka gabatar. Mu ci gaba da yaƙi da mummunar ɗabi'ar."

Zurfafa fahimtar addini

Ta ƙara da cewa: "Na lura cewa ya kamata UNESCO ta yi aiki daidai da ƙudurorin Majalisar Dinkin Duniya kan wannan batu. An yarda da daftarin shawarar tare da gyare-gyaren da muka gabatar. Ci gaba tare da gwagwarmayar yaƙi da laifukan ƙiyayya."

Ayyukan wulaƙanta Ƙur'ani a Turai sun haifar da muhawara game da juriya ta addini da 'yancin fadin albarkacin baki, wanda ya haifar da kiraye-kirayen a zurfafa fahimtar ra'ayin addini da kuma sake yin la'akari da daidaito tsakanin 'yancin fadin albarkacin baki da mutunta akidar addini.

A watan Yulin 2023, babban taron Majalisar Dinkin Duniya baki daya ya amince da wani ƙuduri da kasar Maroko ta dauki nauyin gabatarwa wanda ya kira ayyukan cin zarafi ga alamomin addini da litattafai masu tsarki, da wuraren ibada da suka saba wa dokokin kasa da kasa.

TRT World