Duk mutum biyar din da ke cikin jirgin, har da matukin jirgin Stockton Rush, "abin bakin ciki duk sun bata."/ Hoto: AFP

Wani jirgin ruwa mai nutsewa a karkashin teku da ke dauke da mutum biyar zuwa wajen da tarkacen jirgin Titanic yake ya tarwatse tare da kashe duk mutum biyar da ke cikinsa, a cewar jami'an Amurka.

Hakan ya jawo tashin hankali da kawo karshen neman jirgin da ake yi ba dare ba rana a fadin duniya.

A wajen wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Alhamis, jami'an gadin gabar teku na Amurka sun ce sun ankarar da iyalan mutanen da ke cikin jirgin na Titan, wanda ya bata tun ranar Lahadi.

Sai dai fatan da ake da shi na ganin jirgin, mai dauke da mutum biyar duk maza, ya gushe a ranar Alhamis bayan iskar oksijin din jirgin mai tsawon awa 96 ta kare, kuma hukumar gadin gabar tekun ta sanar da cewa an gano tarkacen jirgin can a nisan kamu 1,600 daga wajen da Titanic yake a Arewacin Tekun Atlantika.

"Wannan tarwatsewa ta jirgin nan abin tashin hankali ne sosai," in ji Rear Admiral John Mauger na hukumar masu kula da gabar teku ta First Coast Guard District.

Kamfanin OceanGate Expeditions, mamallakin jirgi marar nutsewar, ya ce a cikin wata sanarwa cewa duk mutum biyar din da ke cikin jirgin, ciki har da shugaban kamfanin kuma matukin jirgin Stockton Rush, "abin bakin ciki duk sun bata."

Sauran mutanen da ke cikin jirgin sun hada da wasu mutum biyu daga wani shahararren iyali na Pakistan, Shahzada Dawood da dansa Suleman Dawood; da wani dan Birtaniya mai bincike Hamish Harding da kuma wani kwararre kan sha'anin jirgin Titanic Paul-Henri Nargeolet.

"Wadannan mutanen masu bincike ne na ainihi da suke da tsananin sha'awar kare tekunan duniya," a cewar kamfanin OceanGate a wata sanarwa.

"Mun yi bakin cikin rashinsu kuma muna jimamin irin farin cikin da suka dasawa kowa."

Gwamnatin Pakistan a ranar Juma'a ta mika ta'aziyya ta musamman ga iyalan uba da da 'yan kasar tata.

Ma'aikatar Harkokin Wajen kasar ta ce "Muna mika sakon ta'aziyyarmu ga iyalan Dawood da na sauran fasinjojin cikin jirgin a bisa labari marar dadi na abin da ya faru ga jirgin Titanic marar nutsewa a cikin Arewacin Tekun Atlantika."

Ci gaba da bincike don gano abin da ya faru

Tun shekarar 2021 Kamfanin OceanGate yake ta adana bayanai kan rubewar da jirgin Titanic yake yi ta hanyar zuwa wajen duk shekara, da damuwa kan yadda hakan ke shafar halittun cikin ruwa da ke kusa da shi.

Masu aikin ceto sun yi ta hanzarin aike jiragen ruwa da jiragen sama da sauran kayan aiki zuwa wajen da jirgin ya bace.

Hukumomi sun yi fatan karar da aka ji a can karkashin ruwa a ranar Talata da Laraba ka iya taimakawa wajen gano wani abu a kurkusa, bayan da yankin da ake binciken ke da fadin dubban mila-milai – da girmansa ya fi yankin Connecticut na Amurka zurfinsa kuma ya kai kilomita hudu.

Amma masu kula da gabar teku a ranar Alhamis sun ce da alama karar da aka jiyo din ta wani abu ce daban ba ta jirgin Titan ba.

“Ba a ji kamar akwai alaka tsakanin karar da aka ji ba da kuma wajen da tarkacen jirgin yake a can karkashin tekun,” in ji Mauger.

Mauger ya ce ya yi wuri a ce za a gano ko jirgin ya tarwatse ne jim kadan bayan maganar da aka yi da mutanen da ke cikinsa a ranar Lahadi.

Hukumar Kula da Gabar Teku za ta ci gaba da bincike a kusa da Titanic din don sake gano alamun abin da ya faru ga jirgin Titan.

Kazalika Mauger ya ce za a ci gaba da kokarin gano gawarwakin mutum biyar din da duk suka mutu.

Jirgin Titan ya fara balaguronsa ne a tekun ranar Lahadi da misalin karfe 6 na safe agogon Amurka, aka kuma ba da rahoton cewa ba a ganshi ba da rana, daga nisan kilomita 700 daga kudancin St. John da ke Newfoundland.

Jirgin ya tashi ne da nufin zuwa wajen da jirgin Titanic ya nutse fiye da shekara 100 da suka wuce.

Zuwa ranar Alhamis kuwa da ake tsammanin saura kiris iskar da suke shaka ta oksijin ta kare, sai aka fara fitar da ran gano mutanen da ke cikin jirgin a raye.

TRT World