A kalla mutum 20 ne suka mutum sakamakon wani mummunan harsarin mota da ya rutsa da su a kasar Saudiyya.
Wata sanarwa da shafin da ke kula da Masallatai Biyu Masu Daraja, na The Holy Mosques ya wallafa a Tuwita ranar Talata da safe, ta ce mutanen maniyyata Umara ne.
Baya ga wadanda suka mutu kuma wasu mutum 29 sun jikkata a hatsarin wanda ya faru a garin Aqaba Shaar da ke gundumar Asir ranar Litinin da yamma.
Sanarwar ta ce hatsarin ya faru ne sakamakon karon da babbar motar safa mai dauke da mahajjatan ta yi da wata babbar gada.
"Yin karon ke da wuya sai motar ta wuntsila sannan ta kama da wuta," kamar yadda The Holy Mosques ya wallafa.
Mahajjatan suna kan hanyarsu ta zuwa Makkah ne don gudanar da ayyukan Umara a cikin wannan wata na Ramadana.
Hukumomin tsaro da na ba da agaji sun yi gaggawar zuwa wajen don ayyukan ceto, kamar yadda rahotanni suka ambato.
Tuni aka kai gawar mamatan da ta wadanda suka jikkata zuwa asibitocin da ke yankin.