Akalla mutum dubu 650,000 ne suka rasa rayukansu a cikin shekaru 50 da suka gabata sakamakon fari a kasashen duniya daban-daban.
Masana na bayyana cewa a ‘yan shekarun nan an samu karuwar fari a sassan duniya daban-daban.
Fari na nufin daukar wani tsawon lokaci ba tare da an yi ruwan sama ba.
A wasu yankuna na duniya akan dauki tsawon watanni ko shekaru ba tare da an samu saukar ruwan sama ba lamarin da ke janyo bushewa da kekashewar kasa.
Masana sun kuma bayyana cewar abubuwan da ke janyo fari sun hada da tsananin zafi, sauyin yanayi, karuwar jama’a da bukatuwa ga ruwa, sare itatuwa da raguwar ingancin kasa.
Nan da shekarar 2030 karancin ruwa ko fari zai shafi kaso arba’in cikin dari na al’ummar duniya. Karancin ruwa na illa da tasiri kan tattalin arziki da rayuwar mutanen yankunan da ibtila’in ke shafa.
Kazalika rashin ruwa na janyo bushewar kasa da dazuka wanda ka iya janyo gobarar daji, mutuwar dabbobi da rashin tsirowar amfanin gona, wanda hakan ke haifar da yunwa saboda karancin abinci a duniya.
Fari na kuma janyo rashin tsaftar muhalli wanda hakan ke janyo cututtuka irin suwa kwalara da salmonella.
Sannan wata illa da masana suka bayyana fari na iya janyo wa ita ce tilasta wa mutane da dabbobi yin hijira daga yankunan da ake fama da fari zuwa wuraren da suke da ruwa.
Ana iya magance afkuwar fari ta hanyoyoyin tattalin ruwa a gidaje, gonaki da wuraren ayyuka. Sannan shuka bishiyoyi ma na taimaka wa wajen hana afkuwar fari.