Duka mawaƙan sun bayyana farin ciki da kyakkyawan fata kan wannan sabon aikin. Hoto : Davido/ Kidjo Instagram 

Fitaccen mawaƙin nan na Nijeriya da kuma fitacciyar mawaƙiya Angelique Kidjo sun sake haɗa kai, a wannan karon domin fitar da sabuwar waƙa da aka yi wa laƙabi da "Joy."

Waƙar, wacce aka shirya sakinta a ranar 30 ga Agustan 2024, "Joy" na nuna ci gaba da aiki tare domin samun nasarar haɗin kan da suka yi a baya wajen sakin waƙar "Na Money."

Duka mawaƙan sun bayyana farin ciki da kyakkyawan fata kan wannan sabon aikin, suna bayyana ta a matsayin sabuwa waƙa ta musamman da ke da muhimmanci a gare su.

"Abin farin ciki ne yin aiki da gwarzo @angeliquekidjo a kan JOY," kamar yadda Davido ya rubuta a Instagram.

"Na gode ma @davido saboda kawo haskenka! Ba wanda zai yi fiye da abin da ka yi. Muna fata wannan waƙa za ta haɗa kan duniya na wani lokacin domin samun "farin ciki," in ji Kidjo a Instagram.

Ƙwarewa ta daban wurin waƙa

Masu sharhi na san ran cewa wannan haɗakar za ta zama wani lamari na daban a tarihin waƙa, idan aka kwatanta irin kiɗan Davido na Afrobeat da irin waƙoƙin da Kidjo ke yi.

Duk da cewa babu wani sharhi da aka yi kan "Joy", haɗin gwiwar da suka yi a baya an jinjina mata sakamakon yadda karin waƙar yake da kuma amfaninsa ga al'ada.

Dangane da ayyukan da suka yi a baya da kuma yadda aka karɓi waƙarsu ta "Na Money," an yi hasashen cewa "Joy" za ta kasance wata babbar haɗin gwiwa wadda za ta nuna iko dangane da musayar al'adu.

Jigon waƙar wanda shi ne jin daɗi da haɗin kai kamar yadda Kidjo ta bayyana, akwai tabbacin masu saurare a faɗin duniya za su ji daɗinta.

Da waƙar "Joy," Davido da Angelique Kidjo na ci gaba da faɗaɗa waƙa a Afirka, inda suke bayar da sabbin waƙoƙi masu daɗi waɗanda ke ɗaukaka al'adun gargajiya.

TRT World