Labaran karya na ci gaba da yaduwa game da zaben Turkiyya, inda a baya-bayan nan aka kirkiro maudu’ai na bogi don jefa fargaba lokacin girgizar kasar 6 ga watan Fabrairu da kuma kokarin da ake yi na kai wa mutanen da lamarin ya shafa agaji.
Jami’ai da masu zabe a Turkiyya sun bayyana fargabarsu kan masu watsa labaran na bogi game da zaben 14 ga watan Mayu da kuma irin tasirin da hakan zai yi.
Tuni suka tabbatar da wadanda ke assasa wannan lamari.
Wani labarin karya da aka kirkiro game da yanayin koshin lafiyar shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sanya rudani kuma ya ragu ne bayan Daraktan Sadarwa na kasar ya fitar da sanarwa inda ya fayyace gaskiyar lamarin.
A gefe guda, kafafen watsa labaran kasar sun bayar da rahoton wasu gungu shida "na masu watsa labaran karya" inda suka kirkiro shafukan bogi 121 kuma suna aiki ne da yawun jam’iyyar hamayya ta CHP.
Ana zargin wadannan shafukan sada zumunta da yada labaran karya da na kiyayya ga wasu kabilu da kuma sanya wa mutane shakku game da sahihancin zaben da ke tafe.
A koyaushe, wadannan shafukan sada zumunta suna sake rarraba bayanan da junansu suka wallafa domin samun karin jama’a da kuma jan hankalin mutane masu dimbin yawa.
Suna kuma sassauya sunan shafukansu da kuma bayanan da suke wallafawa domin yin bad-da-bami da zummar samun amincewar karin jama’a daga bangarori daban-daban.
Samuwar shafukan sada zumunta
Samuwar shafukan sada zumunta ta zo da damarmaki da kuma sabbin kalubale wajen sadarwa, musamman yadda ake watsa labaran karya.
Haka kuma ta sa kasashen waje suna yin katsalandan a zabukan wasu kasashe lamarin da kan shafi ra’ayin ‘yan kasa a yayin kada kuri’unsu.
Wasu daga cikin katsalandan din da kasashen waje suka yi sun faru ne a game da zabukan Amurka da Kenya da kuri’ar jin ra’ayin jama’a kan ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai wato Brexit.
Hakan ya dasa babbar alamar tambaya game da rawar da ‘manyan kamfanoni’ na sada zumunta suke takawa.
Wasu bayanai da aka fitar game da "Shafin Twitter" sun nuna irin rawar da manyan shafukan sada zumunta suke takawa don sauya ra’ayoyin jama’a a zabukan kasashe.
Shafukan bogi suna iya yin gaggawar watsa bayanan karya da zummar sauya akiblar zabukan kasashe.
Hakan ne ya faru yayin da aka zargi kamfanin Cambridge Analytica da yin amfani da miliyoyin shafukan Facebook na masu zabe a Amurka don yin tasiri a zaben kasar na 2016.
Shi kansa shugaban Meta, Mark Zuckerberg, ya yarda cewa ana amfani da kamfaninsa don watsa labaran bogi.
"A bayyane take cewa mun gaza yin abin da ya kamata domin magance wannan matsala ta watsa labaran bogi musamman a shekarun baya bayan nan," in ji shi.
"Hakan ya sa ana samun karin labaran bogi da katsalandan na kasashen waje a zabuka da makamantansu."