Mbappe

A yau Alhamis ne Sashen shari’a na Hukumar Ƙwallon Ƙwararru ta Faransa, ya zartar da hukuncin kan ƙorafin da Kylian Mbappe ya yi cewa yana bin tsohon kulob ɗinsa, Paris Saint-Germain bashin albashinsa euro miliyan €55 (dala miliyan $61).

Wannan mataki na zuwa ne kwana guda bayan Mbappe ya yi watsi da tayin da hukumar ta masa na ya zauna teburin sulhu da tsohon kulob din nasa don warware takaddamar.

Hukumar ƙwallon ta Faransa ce ta sanar da kamfanin dillancin labarai na Associated Press, wanna hukunci, amma bai ba da cikakken bayani ba.

Jami’an kungiyar ta PSG sun zauna da wakilan Mbappe a birnin Paris ranar Laraba, bayan da Mbappe ya nemi hukumar ta shiga tsakani. A wannan bazarar ne Kylian Mbappe ya koma taka leda a Real Madrid bayan barin PSG.

Bayan zaman da suka yi, wakilan Mbappe sun fada wa AP cewa dan wasan ya nemi hukumar ta duba batun albashinsa na watanni uku da sulusin bonos dinsa da ba a biya ba.

Sai dai PSG ta ce ba ta da niyyar biyan wadannan kudade, inda ta sanar da cewa za ta dauki matakin na gaba, na daukaka kara.

Kulob din ya sanar da cewa, “Duba da takaitar karfin shari’a na hukumar na daukar cikakken mataki kan batun, don haka dole a yanzu a kalubalanci batun a wani fagen shari’a, wanda PSG ta dauki aniyar gabatar da bayananta cikin watanni masu zuwa”.

TRT Afrika