Hotunan Nnadi na bayyana tsagwaron kaunar da ke tsakanin iyaye mata da 'ya'ya mata. Hoto: Ikechukwu Nnadi

Daga Pauline Odhiambo

Idan kalmomin magana ba za su isa ba wajen bayyana soyayyar da ke tsakanin uwa da 'ya, watakila zane zai fi iya bayyana wannan kusanci mai karfi. Wannan ne abinda mai zanen dan Nijeriya Ikechukwu Nnadi ya yi amanna da shi.

Bayan an haifar masa 'ya mace, Nnadi ya fara tunanin zana hotunan d ake bayyana kauna da ke tsakanin uwa da 'ya mace.

"Bayan samun labarin matata za ta haifi mace ya sauya min rayuwa. Hakan ya sanya ni fara zuzzurfan tunanin irin so da kaunar da ke tsakanin uwa da 'ya, na kuma bayyana shi a zanen da nake yi," Nnadi ya fada wa TRT Afirka.

A yanzu haka yana aiki kan zane guda takwas da zai bayar da jimillar hotuna 12.

Zanen da Nnadi ke yi ya samu ne daga tunani zuwa tabbas. Hoto: Nnadi

‘Kyakkyawan Hoto’

Amma kuma sawwara alakar so d akaunar ya zama babban jigon sana'ar ta Nnadi. Ya samu ilhamar yin daya daga zanensa daga mahaifin wanda mai daukar hoto ne da ke aiki da tsabaki.

"A lokacin ina karamin yaro, na yi yunƙurin zana hoton mahaifina, sai na yi ta yin zane da yawa ta hanyar kallon hotonsa," in ji mai zanen dan shekara 34.

"Na yi ta zana hoton sau shurin masaki har sai da na yi daidai da yadda yake a zahiri."

Wannan yunkuri na ganin ya fice ne ya sanya shi fara zane-zane - basirar da ya karfafa lokacin yana sakandire da jami'a.

The perceived emotional states of the subjects makes the paintings relatable to a viewer . Hoto: Nnadi

Ya ce "Na fara sayar da hotona na farko ga kawar 'yar uwata a lokacin ina makarantar sakandire. Biya na kudi kan abinda na ke kauna ba karamin karfafa min gwiwa ya yi ba saboda hakan ya taimake ni wajen kashe kudade a jami'a."

‘Mai zane da gaske’

Salon zanensa ya habaka sosai, a hankali ya dinga sauya salo daga dan koyo zuwa kwararre yadda yake a yanzu. "Ya dauke ni shekaru da dama ina ta zane don habaka tsarin zane na," in ji matashin da ya yi karatun zane a jami'a.

"A baya ina kiran kaina da mai koyon zane, amma a yanzu na zama cikakken mai zane, saboda a yanzu hotuna na isar da sakon wadanda ke jikin hoton ta hanyar isar da halin da suke ciki ga jama'a."

Tasirin na kusa da fahimtar halin da wanda ke jikin hoton ke ciki, wanda ke sanya zanen ya zama kamar na gaske a zuciyar mai kallo.

'Hoton Mace' jerin hotunan ne da nuna mata a cikin yanayi daban-daban suna raba daya biyu. Hoto: Nnadi

"Har a lokacinda na smaar da tsarin zana hotunana, na fara ba su damar zama a tsayayyen yanayi tare da rasa me zan ce ta yadda zan fi samun damar gano halin da suke ciki," in ji Nnadi.

"Na yi kokarin suranta yadda na ke son su kasance tare da hada su da labaran da na ke da su a zuciyata. Wannan wani abu ne da na ke son mutane su gani a loakcinda suka kalli hotunan da na zana."

'Takardar Zane Mai Tsada'

Haka zalika wani salon zane da Nnadi ke yi shi ne 'Hoton Mace' da ke nuna mata daban-daban a cikin mabambantan yanayin tunani.

Ya kuma zana wano hoton kansa da ma wani jerin hotuna mai taken Anwulika wanda a yaren Igbo ke nufin 'farin cikina na da yawa'.

'Anwulika' na nufin 'farin cikina na da yawa' a yaren Igbo. Hoto: Nnadi

Farin cikin Nnadi na zane watakila ya ta'allaka ne ga irin farashin da wasunsu suke da shi.

"Yana da wahala samun ingantacciyar takarda, hakan ya sa dole na ke sayo takardadta daga kasashen waje a farashi mai tsada," in ji shi.

"Ana kawo min takardar a na ke zane a kanta daga kasashen waje, hakan ya sanya zanen nawa ke da tsada shi ma."

A wasu lokutan ma Nnadi na sayo karin wasu kayayyakin daga kasashen waje.

‘Aminta da sana'a’

"Ina fatan kamfanonin da ke samar da wadannan kayayyaki na zane wata rana za su bude shaguna a Nijeriya wand ahakan zai rage farashinsu," in ji shi yana cikin murmushi.

"Ya kamata su fara tunanin saka masu zane na yankuna a matsayin jakadun kayayyakinsu ta yadda masu zanen za su samu rangwamen kayan da suke bukata."

An baje-kolin hotunan Nnadi a Nijeriya da Faransa. Hoto: Nnadi

An yi baje-kolin hotunan Nnadi a gida Nijeriya da kasar Faransa a lokacin bukuwa.

Shawarar Nnadi ga masu zane da ke tasowa: "Ku amince da sana'arku ku ci gaba da kyautata ta. Ka bawa kanka jin cewar kana kuskure. Wadannan kura-kurai za su taimaka maka wajen zama mutumin da kake son zama."

TRT Afrika