Daga Tooba Masood Karachi, PAKISTAN
Matakin da Tik Tok ya ɗauka kwanan nan na haramtawa ƙananan matasa ƴan ƙasa da shekaru 18 yin amfani da manhajar ƙara kyau na iya fusata wasu matasan, amma masana a fannin tasowar yara da kuma kwararru a fannin kiwon lafiya sun ce ya zo a kan gaɓa kuma mataki ne da ya dace.
Daga shekara mai zuwa, kafar bidiyon na ɗan takaitaccen lokaci, wadda ke da masu amfani da ita fiye da mutum biliyan ɗaya, za ta hana ƙananan matasa yin amfani da manhajar ƙara kyau kamar Bold and Glamour, wacce take amfani da manhajar AI ta yi matuƙar sauya kamannin mutum.
"Sanannen abu ne yadda ƙananan matasa da ke matakin balaga suka ɗauki batun irin kallon da suke yi wa kansu, kuma a galibin lokaci suna kwatanta kyaunsu da na wasu.
"Saboda haka,kafofin sada zumunta ba su da wani tasiri kan tunanin yaro mai tasowa," a cewar Dr Tania Nadeem, likitan ƙwaƙwalwa a sashen ƙananan yara da yara masu tasowa a Asibitin Jami'ar Aga Khan.
"Idan kafofin sada zumunta suka tallata wannan nau'in cikar halitta ko ƙurewar kyau kamar yadda ake faɗa, daga nan sai ƙananan matasa su fara kwatanta kyaunsu da wannan ƙurewar kyaun, idan kuma kyaunsu bai kai wannan ba, sai hakan ya haifar da mummunan yanayin da za su dinga kallon kansu."
A tsawon ƴan shekarun da suka gabata, ana nuna damuwa game da mummunan tasirin manhajar ƙara kyau ta Tik Tok kan tunani, musamman kan ƙananan ƴan mata.
Waɗannan ƴan matan suna nuna damuwa da sai sun yi ɗan karen kyau a kodayaushe, kuma wani lokaci suna raina kyaunsu na asali bayan sun yi amfani da manhajar ƙara kyau.
Matakin na Tik Tok ya biyo bayan wani binciken kasuwanci da ya gudanar tare da kungiyar sa-kai ta Birtaniya Internet Matters.
Binciken ya yi nazari kan rawar da kafofin sada zumunta ke takawa wajen shata asali da kuma dangantakar ƙananan matasa.
Ɗaya daga cikin manyan batutuwa da aka lura da su shi ne damuwar da ƙananan matasa da iyaye suka nuna kan tasirin yadda mutum ke fita, har da yiwuwar cewa waɗanda suke kallon hotunan da aka samar ta manhajar ƙara kyau wataƙila ba za su fahimci an jirkita su ba.
Yaudarar ta manhajar ƙara kyau ta yi ƙamarin da hatta manya ma ta shafe su. Wani binciken da jami'ar City of London ta gudanar daga shekarar 2020 ya gano cewa kashi 99 na matasan mata suna yi wa hotunansu kwaskwarima saboda sun damu su ga cewa sun kai matakin ƙurewar kyau da ake yayi.
Manhajar ƙara kyau kamar ta Bold and Glamour ta bai wa masu amfani da Tik Tok su ƙara wa idanuwansu girma ko su ɗan tsuke hancinsu, su ƙara wa fatarsu haske, ko kuma su ɗan ƙara tudun laɓɓansu fiye da yadda suke.
Abin da ake yayi
Dandalin Kafofin sada zumunta sun samu gagarumin sauyi a baya bayan nan.
Australia ta gabatar da ƙudurin dokar da za ta haramta wa ƙananan matasa ƴan ƙasa da shekara 16 yin amfani da kafofin sada zumunta kamar Tik Tok da Instagram, abin da ya sa ta zama ƙasa ta farko da ta buƙaci a ɗauki wannan tsattsauran matakin.
Wasu ƙasashen har da Albenia suna duba yiwuwar ɗaukar irin waɗannan matakan.
Roblox, wani shafin caca wanda ke da masu amfani da shi a kullum miliyan 90, ya sanar da sabbin matakai domin kare masu kananan shekaru daga cikin masu amfani da shi daga abubuwa masu nasaba da tashin hankali da ƙeta da abin tsoro da kuma cin zarafi ta yanar gizo.
Instagram ya gabatar da "shafin ƙananan matasa" domin masu amfani da shi ƴan ƙasa da shekaru 18 da haihuwa, domin bai wa iyaye damar saka ido da kuma sarrafa al'amurra.
Dr Humair Yusuf, wani farfesan ilimin tunanin ɗan'adam a Jami'ar LUMS ta Pakistan,yana cewa manhajojin ƙara kyau kamar na Tik Tok da Snapshot suna shafar lafiyar tunanin matasa matuƙa gaya, kuma ya goyi bayan shirye shiryen hana su yin mu'amala da su.
"Amma kuma, ana addabar ƙananan matasa da batun ƙurewar kyau ta fuskoki da dama da rufe ƴan wasu manhajoji ba dole ne ya yi wani tasiri ba," ya sheda wa TRT World.
Yin mu'amala da hotuna da manhajar ƙara kyau ta samar wanda masu amfani da ita suka yi kyau sosai kuma ba su da makusa yana yin lahani ga haiba da kuma lafiyar tunanin matasa, in ji ƙwararru.
"Ko shakka babu yana ta'azzara ƙawazuci kuma wani lokacin ya haifar da matsalar zamantakewa," in ji Tania Nadeem ta Asibitin Jami'ar Aga Khan.
"Ko da a wajen yara da ke matakin balaga waɗanda suke jin cewa sun kai matakin ƙurewar kyau, zai ƙara musu halayyar yaba kansu da kansu ne kawai sannan kuma ya karfafa mayar da hankali kan shiga ta zahiri a maimakon ɗabi'u kamar tausayi ko kirki."
Ba ƙaramin aiki ba ne
Kamfanonin samar da dandalin sada zumunta da masu zuba ido kan lamuransu suna da sauran aiki da yawa a gabansu wajen kare ƙananan yara daga lamura masu hatsari da kuma manhajoji.
Alal misali, kafin Tik Tok ya iya dakatar da ƴan ƙasa da shekaru 18 daga amfani da manhajar ƙara kyau, wajibi ne kamfanin ya san ainihin shekarunsu. Wasu yaran suna buɗe shafuka ba tare da bayyana ainihin shekarunsu na haihuwa ba.
Tik Tok ya ce yana amfani da fasahar zamani ya kintaci shekarun mutum. A cewar shafin yanar gizo na Tik Tok, " Idan ka zaɓi ka yi amfani da kintatar fuska ka tabbatar da shekarunka a Tik Tok, muna aiki da Yoti, wata na'ura da take tantance shekaru, mu yi ƙiyasin shekarunka ta hanyar amfani da bayanan fuskarka da aka samu daga hoton selfie da ka gabatar".
Tik Tok ya dage cewa zai yi amfani da fasahar koyo domin kyautata ƙoƙarinsa na hana yara ƴan ƙasa da shekaru 13 su yi amfani da dandalin.
Amma Nadeem ya ce daga ƙarshe, aikin manya ne, iyaye - malamai - waɗanda suke taimakawa wajen dasa kwarjini tsakanin matasa da kuma cusa ƙarin muhimman ɗabi'u.
"Za mu iya magana a kan waɗannan abubuwan a makaranta da kuma muhimman kyawawan ɗabi'u kamar aiki tuƙuru, gaskiya da kuma tausayi fiye da kyaun mutum. Amma na yi imani taƙaita waɗannan manhajojin mataki ɗaya ne kawai.