Exodus ya ce yana da burin taimaka wa mutane bayan ya yi fama da matsalar damuwa. Hoto: Shafin instagram na Exodus

Mawaƙin bishara ɗan asalin ƙasar Uganda George Lubega Timothy da aka fi sani da Exodus kana ya lashe lambobin yabo da dama, ya bayyana godiyarsa ga irin goyon bayan da ya samu bayan labarin da ya bayar na gwagwarmayarsa da matsalar damuwa.

A cikin watan Maris ne mawaƙin ya bayyana cewa ya yi ta fama da matsalar damuwa tun daga shekarar 2013, bayan mutuwar mahaifiyarsa.

Mawaƙin mai shekaru 40 ya rubuta a shafinsa na Instagram cewa yana mika godiyarsa ga ɗaukacin mutanen da ''suka saurare ni game da wayar da kai kan lafiyar ƙwaƙwalwa a Uganda.''

''Ina maraba da kowannen ku da ke son mu haɗa kai wajen yakar wannan annoba yayin da muke ƙokarin kawar da rashin yin magana kan yawan matsalar ƙwaƙwalwa a Uganda.'' in ji shi a cikin sakonsa na Instagram.

Babban Rashi

Exodus ya ce ya ɗauki hutun yi waƙa amma ya samu kwanciyar hankali ta hanyar shan barasa da ƙwayoyi da suka kusan halaka shi.

Exodus mawaƙin bishara ne daga ƙasar Uganda da lashe lambobin yabo da dama.Hoto: shafin Instagram na Exodus

"Fadi tashina ya fara ne a cikin 2013 lokacin da na rasa mahaifiyata abar ƙaunata. A lokacin, mun gano cewa tana da ciwon daji a mataki na hudu. Lokacin da ta mutu, na rasa aikina da gidana, da motocina," in ji Exodus a cikin wata sanarwa a watan Maris.

Bayan zama a cibiyar gyaran tarbiyya, Exodus ya ce yanzu ya samu ƙwarin gwiwar son taimaka wa wasu da ke cikin irin wannan yanayi.

"Ina kan fafutukar wayar da kan jama'a domin su iya sanin mece ce lafiyar kwakwalwa ko batutuwan da suka shafi tunani da damuwa.

Matsalolin lafiyar ƙwaƙwalwa

Exodus ya lashe Kambin gwarzon Mawaka Maza a rukunin Wakokin 'Groove and Olive Gospel' a kalla sau 10, kuma bayaninsa game da lafiyar kwakwalwa ya samu karbuwa a wajen matasa Uganda da dama.

Kungiyar Kula da Halayyar Dan Adam ta Amurka ta ce Uganda na daya daga cikin kasashen Afirka shida da ke kan gaba wajen samun masu fama da cutar damuwa da yawa.

Ma'aikatar lafiya ta Uganda da Kungiyar Bayar da Shawarwari ta Uganda sun kara da cewar akwai kimanin 'yan kasar miliyan 14 da ke fama da wani nau'i na cutar kwakwalwa da tunani.

"Mutane da dama na fama da irin wannan kalubale amma suna tsoron fito wa su bayyana saboda irin fahimtar da jama'a za su yi musu, musamman a masana'antar mawaka. Batun ciwon hankali ko kwakwalwa annoba ce ta duniya baki daya da ba mu rungume ta don magancewa ba har yanzu," in ji Exodus.

TRT Afrika